Kungiyar sintiri ta Amotekun da ke jihar Ondo tare da hadin Gwiwar sauran Jami’an tsaro sun tabbatar da kama wasu daga cikin ‘yan Bindigar da suka kai hari a Cocin St. Francis da ke a yankin Owo, cikin jihar Ondo.
Jami’an sun kuma kwato wasu malamai tare da wata mota da maharan suka yi amfani da ita wajen kai harin.
Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa, a lokacin harin na ranar 5 ga watan Yunin 2022, masu gudanar da ibada guda 40 ne ‘yan Bindigar suka kashe, inda kuma Da dama, suka samu raunuka.
Kwamandan na Amotekun, Akogun Adetunji Adeleye ne ya bayyana hakan a lokacin da suka Bayyana ‘yan Bindigar tare da sauran wasu masu laifi da suka kama.
Ko da yake, Akogun bai bayar da cikakken bayani da kuma adadin ‘yan Bindigar aka kama da suka kai harin a Cocin ba, amma ya sanar da cewa, sauran Jami’an tsaro na ci gaba da kokarin kamo suka asauran wadanda aikata ta’asar.
Ya ci gaba da cewa, kungiyar ta kuma yi bajin kolin masu garkuwar guda da mutane su 71 da take zargi da masu fashi da makami da masu kwatar baburan da ake yin Achaba da kuma masu yin safafar mutane.
A cewar Adeleye, sun kama mutane da dama dangane da hare-haren biyu, inda ya kara da cewa a cikin kwana daya, sun kuma kwato baburan Achaba guda 30 da aka sace.