Shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Mele Kyari, ya ce mutane da dama a Nijeriya na da hannu wajen satar danyen man da ke hakowa, bayan da suka gano famfo sama da 5,570 da ake amfani da su wajen satar danyen mai.
Kyari ya bayyana haka ne ga kwamitin majalisar dattawa na musamman da ke bincike kan matsalar satar mai, ya ce a cikin shekara guda kawai sun gano yadda aka fasa bututun har sau 9,000 domin satar danyan man.
- Mun Shiga Yaki Da Masu Satar Mutane – Remi Tinubu
- An Gudanar Da Taron Tattaunawa A Tsakanin Kafofin Watsa Labaru Na Kasa Da Kasa Mai Taken “Sin A Lokacin Bazara” A Amurka
Shugaban kamfanin ya ce daga shekarar 2022 zuwa wannan lokaci, NNPC ya lalata haramtattun matatun man da ake amfani da su wajen tace man sata.
Kazalika, ya bayyana cewar a tsakanin wannan lokaci sun gano wurare 5,570 da aka dasa kan famfo daga bututun man ana sata, yayin da suka yi nasarar cire 4,876 daga cikinsu.
Shugaban kamfanin, ya ce wasu daga cikin irin ta’addancin da suke gani ake yi wa bututun man hankali ba zai iya dauka ba, yayin da su kuma ba su da karfin da za su iya dakile shi, ganin yadda ake musu zagon kasa wajen sake fasa bututun da zarar sun katse na satar.
Kyari ya ce wasu daga cikin wadannan wuraren da ake satar man na kusa da garuruwa, wasu kuma ba su wuce mita 100 daga cibiyar tace man ba.
Kyari ya ce kamfanin na da karfin samar da ganga miliyan biyu na danyen mai a kowace rana, amma satar man na musu zagon kasa, abin da ya sa a yanzu ganga miliyan daya da dubu 600 kawai suke iya samarwa.