Sanata Ali Ndume, ya bayyana cewar sun ja hankalin Shugaba Tinubu kan yadda tsadar kayan abinci ke barazana ga rayuwar al’ummar Najeriya.
Ndume, a hirarsa da BBC, ya bayyana cewa babbar matsalar da ake fama da ita a wannan gwamnati ita ce kofarsu a rufe ta ke yadda hatta wasu ministocin ba sa iya ganin shugaban kasa, bare ‘yan majalisa.
- Kaf Nijeriya Cikin Filayen Jiragen Sama Fiye Da 22, 3 Ne Kacal Ake Cin Riba – FAAN
- Har Kullum Babbar Kasa, Ita Ce Mai Kulawa Da Kanana
Sanatan na magana ne jim kadan bayan sun gabatar da wani kudirin hadin gwiwa tsakaninsa da takwaransa Sanata Sunday Steve Karimi, suna cewa hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaÉ—in mutane miliyan 82 za su yi fama da matsalar abinci a Najeriya nan da shekara biyar masu zuwa.
Sanata Ndume ya ce manufar kudurin ita ce, janyo hankalin mahukunta su san matsalar yunwar da ake fuskanta a Najeriya baki daya.
Ya koka matuka kan yadda ake rayuwa a yanzu, lamarin da ya ce idan ba a yi da gaske ba al’amura na iya lalacewa.
Ire-iren wannan kiranye-kiranye an sha yin su ga shugaban kasa da gwamnoni kan illar da ke tattare da tsadar kayan abinci.