Hukumar kashe gobara ta kasa da ke kula da shiyya ta daya a Jihar Kaduna ta fitar da rahotannin matsalolin gobara da suka faruwa a wannan shiyya guda 87 daga kananan hukumomi takwas, inda suka kashe gobara tare da kare asarar rayukan al’umma maza da mata da kuma dukiyoyin da ba za su misiltu ba.
Babban kwamnadan wannan hukuma mai kula da shiyya ta daya a Jihar Kaduna, Alhaji Aminu Amadu shi ne ya bayyana hakan a lokacin taron bikin cika shekara daya da bude ofishin hukuma a shiyyar Zariya.
Alhaji Aminu ya nunar da cewa sun shirya taron ne domin su yi waiwaye adon tafiya na nasarorin da suka samu daga bude wannan ofishi da kuma gano matsalolin da suka ci karo da su a shekara daya kacal da bude ofishin a Zariya.
Kwamanda ya ce babban nasarar da suka samu sun hada da yadda al’ummar shiyyar Zariya suka fahimci ayyukansu, sannan a wane lokaci da zarar gobara ta tashi a kowace karamar hukuma a shiyya ta daya a kan kira su cikin gaggawa ba tare da wani bata lokaci ba.
A cewarsa, al’ummomin da suke shiyya ta daya sun rungumi ma’aikatan wannan hukuma da hannu biyu ta yadda suke bayar da duk gudunmuwar da suka dace, domin hukumar ta sami damar aiwatar da ayyukan da aka dora su a kai na kashe gobara da kuma wayar da kan al’umma na hanyoyin da ya dace su bi wajen ganin an dakile faruwar gobara a daukacin kananan hukumomin da suke shiyya ta daya a jihar Kaduna.