Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya sanar da rage kashi 70 cikin 100 na ƴan bindiga a cikin shekara guda, inda ya danganta wannan nasarar da haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro na sa kai da suka ɗauka da kuma jami’an tsaro na yau da kullum.
Yayin ziyarar aiki da ya kai Yola, Gwamna Radda ya jaddada buƙatar samar da ƴan sandan jihohi domin su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da rashin tsaro a Najeriya. Ya kuma shaida cewa, yayin da ƴan fashin dajin suka ragu matuƙa, wasu ƴan bindiga sun koma kai hare-hare a ƙauyukan da ke kusa da dazuka, suna ƙona gidaje, da kuma kashe mutane.
Radda ya yi tsokaci kan samar da sabbin dabarun yaƙi da wannan barazanar da ta Kunno Kai, ya kuma jaddada cewa ƙasashe masu tasowa da dama na amfani da ƴan sandan jihohi wajen kare rayuka da dukiyoyi. Daga nan ya yi kira ga Najeriya da ta ɗauki irin wannan matakan.
Bugu da kari, Gwamna Radda ya yi kira ga dukkan masu riƙe da matakan gwamnati da su baiwa ilimi fifiko, domin tabbatar da cewa masu ƙaramin ƙarfi sun samu ingantaccen ilimi, wanda a ganinsa yana da matuƙar muhimmanci ga ci gaban ƙasa.