Hukumar zabe mai zaman kanta a Jihar Kaduna (KAD-SECOM) ta bayyana cewa daga cikin ‘yan takarar shugabancin kananan hukumomin da suka tantance akwai masu tuma’ali da miyagun kwayoyi.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugabar hukumar, Hajiya Hajara Mohammed, a zantawarta da manema labarai jim kadan bayan kammala tantance ‘yan takarar da suka shiga cikin zaben da za a gudanar ranar 19 ga Wotan Oktobar 2024.
- Bangaren Sin Ya Yi Kira Ga Bangarori Biyu Dake Rikici A Sudan Da Su Yayyafawa Rikicin Kasar Ruwa
- Kwalara: Kwara Ta Rufe Gine-gine 14 Saboda Rashin Banɗaki, Ta Gargaɗi Masu Gidaje
Ta ce sun tantance ‘yan takara guda 76 da suka fito daga cikin jam’iyyu 10, tana mai cewa jam’iyyun siyasa 19 hukumar ta yi wa rajista domin shiga zaben, amma guda 10 ne kadai suka tsayar da ‘yan takara.
Shugabar ta ce hukumar ta tsayar da ranar 26 ga wannan watan domin fitar da sakamakon sunayen ‘yan takarar da suka tantancewa. Tana mai cewa sun gudanar tantancewar ne bisa sanya ido daga jami’an ‘yansanda da na hukumar shige da fice ta kasa da hukumar sha da fataucin muyagun kwayoyi da hukumar tara kudaden haraja ta Jihar kaduna.
Hajiya Hajara ta kara da cewa da zarar sun kammala nazari kan takardun ‘yan takarar, za su sanar da wadanda suka samu nasarar tsayawa takarar shugabancin kananan hukumomin jihar.
Ta ce hukumar ta kammala duk wasu shirye-shiryen da suka kamata domin gudanar da zaben kananan hukumomin Jihar Kaduna.
Ta kuma bukaci ‘yan siyasa da su gudanar harkokin yakin neman zabensu cikin lumana da bin dokokin kasa domin samun damar gudanar da zaben cikin nasara kamar yadda aka tsare.