Shugaban Kwamitin Yakin Neman Zaben jam’iyyar PDP a Jihar Adamawa, Awwal Bamanga Tukur, ya ce jam’iyyar ta shirya shiga zaben kujerar gwamna da zai gudana a ranar Asabar.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta sanar da cewa za ta sake zaben kujerar gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihar a wasu cibiyoyi kada kuri’a 78, ranar Asabar.
- Bayern Munich Ta Dakatar Da Sadio Mane
- Xi Jinping: Turbar Zamantarwa Ta Kasar Sin Tana Da Manufa, Tsare-tsare Da Dabaru
Da yake magana a wani taron manema labarai a Yola, shugaban kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar PDP, ya ce “Duk da jam’iyyar PDP ta wuce jam’iyyar APC da kuri’u dubu 31, ba za mu yi wasa da zaben ba.
“Kuri’un da jam’iyyar PDP ta ke dashi ya kai matsayin a ayyana dan takararmu na gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, a matsayin wanda ya lashe zabe, amma INEC ta ce zaben bai kammalu ba, za a sake zaben a cibiyoyi 69.
“Mu mun shirya kamar ba a yi zabe a Adamawa ba, yanzu ne za a yi zaben, muna kira ga jama’a da su ba mu goyon baya mu lashe zaben, jam’iyyarmu ta zama ita ce ta lashe zaben” in ji Awwal.
Haka kuma shugaban kwamitin, ya kuma yi kira ga jama’ar jihar, musamman na wuraren da za a sake zabukan da jama’a su fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri’a, inda ya ce su kuma zabi gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri a karo na biyu.
INEC za ta kuma sake gudanar da zaben kujerun ‘yan majalisar dokokin jihar a kananan hukumomin Numan, Gombi da Girei.