Shugaban Hukumar Zabe ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar hukumar ta shirya tsaf don gudanar da zaben kujerar gwamna a jihar Osun a ranar 16 ga wannan watan.
Shugaban ya sanar da hakan ne a Abuja a wani taro na musamman da hukumar ta yi da kwamatin hukumomin sa ido kan tabbatar da tsaro a yayin zabe, don yin nazari dangane da zaben na jihar Osun.
Hukumar ta ce, wadanda suka kai munzalin jefa kuri’a su guda 1,955,657 ne za su kada kuri’unsu a zaben na ranar 16 ga watan Yulin 2022.
- Mutum Miliyan 1.9 Ne Za Su Kada Kuri’a A Zaben Gwamnan Osun A Watan Yuli – INEC
- INEC Ta Nuna Damuwa Kan Karancin Masu Fitowa Karbar Katin Zabe A Katsina
Kwamishinan da ke kula da ilimantar da masu jefa kuri’a, Festus Okoye, ya bayyana hakan a garin Osogbo a ganawarsa da kafafen yda labarai.
Ya ce, jamiyyu 15 ne za a fafata da su a zaben.
Okoye ya kuma bayar da tabbacin cewa hukumar zata gudanar da sahihin zabe a kujerar ta gwamna.