Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta jaddada cewa, zabukan da za ta sake yi a jihohin Adamawa, Kebbi da sauran jihohi, za a gudanar da su a ranar 15 ga watan Afrilun 2023.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, INEC ta ayyana zabukan gwamna na jihohin Kebbi da Adamawa a matsayin zabukan da ba a kammala su ba, inda hukumar ta ce, za a sake gudanar da zabe a wasu mazabu a jihohin.
Babban jami’in yada labarai na hukumar INEC, Mista Rotimi Oyekanmi ya sanar da hakan a tattaunawarsa da jaridar LEADERSHIP a Abuja, inda ya ce, za a gudanar da zabukan kamar yadda hukumar ta tsara.
Oyekanmi ya ce, tun daga wancan lokacin, babu wani abu da ya sauya.
Leadership ta ruwaito cewa, INEC ta yanke shawara cewa, duk zabukan gwamna da na ‘yan majalisar dokoki da za a sake yi, za a gudanar da su a ranar 15 ga watan Afrilun 2023.
INEC ta dai ayyana zabukan gwamna na jihohin Kebbi da Adamawa da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris na 2023, a matsayin zabukan da ba a kammala su ba, inda ta ce, za a sake gudanar da zabukan a wasu mazabun da ke jihohin.
A jihar Sokoto, daukacin kujerun majalisun tarayya da aka a ranar 25 ga watan Fabrairu, INEC ta ayyana zabukan a matsayin wadanda ba su kammala ba.