Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin zagon ƙasa ta Nijeriya (EFCC), ta sanar da cewa ta shirya tsaf domin yin gwanjon fiye da motoci 850 na alfarma da ta ƙwace a faɗin ƙasar nan.
EFCC ta shaida hakan ne cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X(Twitter), a ranar Litinin, ta ce gwanjon motocin na ƙarƙashin wata dokarta ta 2004 da 2007 da kuma 2022, da suka ba ta damar hakan a binciken da take yi kan ayyukan da suka shaifi laifukan kuɗi da suka haɗa da cin hanci da halatta kudin haram da zamar intanet.
Hukumar ta yi kira ga jama’a da su ci gajiyar gwanjon motocin, wanda ta yi alkawarin za a gudanar kan tsarin adalci a jihar Lages da Abuja da Fatakwal da Kano.
Tuni EFCC ta fitar da adireshin intanet din da za a iya duba motocin da daga yau Litinin 20 ga Janairu har zuwa Litinin ta sama wato 27 ga Janairun 2025, tare da lokutan da za a duba.