Ministan tsaro, Abubakar Badaru, ya roki ‘yan Nijeriya da su yi wa Allah su yi wa Annabi su ci gaba da taimaka wa gwamnati mai ci da tarin addu’o’i na musamman a bangaren tsaron kasa.
Badaru, wanda ya yi wannan rokon a Abuja yayin da ya karbi bakuncin wakilai daga jiharsa ta Jigawa karkashin jagorancin gwamna, Malam Umar Namadi, ya ce, duba da matsalar tsaro da ke addabar Nijeriya, akwai bukatar addu’o’i domin samun nasara a kan matsalar.
- Badaru Na Da Kwarewar Jagorantar Ma’aikatar Tsaro – ANA
- Kungiya Ta Jinjina Wa Tinubu Kan Nada Badaru Ministan Tsaro
A cewarsa, aikin da ke gabansu aiki ne jawur, don haka sun dukufa wajen shawo kan matsalolin kuma akwai bukatar gudunmawa da goyon bayan al’umar Nijeriya ta kowace fuska, ciki har da addu’o’i domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin kasar.
Da ya ke magana tun da farko, gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, da ya jagoranci tawagar sarakuna, shugabannin addinai, ‘Yan kasuwa, ma’aikata da masu ruwa da tsaki daga jihar don kai ziyarar, ya ce, sun kawo ziyarar ne domin taya ministan murna tare da ba shi tabbacin goyon bayansu dari bisa dari a kowane lokaci.
“Ba fa iya zallar mu taya murna ne muka zo ba, a’a mun kuma zo ne domin mu yi maka addu’a. Mun san irin nasarorin da ka cimma a jiharmu, muna maka addu’ar za ka cimma irin wanan nasarar a wannan sabon matsayi da kake kai na ministan tsaro.” Cewar Namadi.
Gwamna Namadi ya tunatar da ministan irin tsammani da fatan da ‘Yan Nijeriya ke yi a kansa na cewa zai yi aiki tukuru domin shawo kan matsalolin tsaron da suke kasar nan, “Muddin ka cimma nasara a wannan bangaren, to kuwa ka taba kowani bangare a fadin kasar.”
“Mun yi nasara kuma mun ci sa’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jiharmu ta Jigawa, hakan ba wai kuma yana nufin ba mu bukatar gudunmawarka ba ne, muna neman taimakonku da gudunmawarka domin ci gaban sauran jihohin kasarmu baki daya,” In ji Gwamnan Jigawa.