Kocin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Mikel Arteta ya bayyana cewar Idan har kungiyar na bukatar lashe kowane irin kofi a badi dole ne su kara karfafa yan wasansu.
Arteta ya yi wannan bayani ne yayin da ake ci gaba da saye da sayarwar ‘yan kwallo a Turai.
Zuwa yanzu dai Arsenal ta dauki dan wasan Chelsea Kai Harvertz inda kuma take dab da daukar Jurien Timber na Ajax da kuma kyaftin din kungiyar West Ham Declan Rice wanda har ila yau ita ma Manchester City ke nema.
Arsenal ta rasa kofin Firimiya na bana a wani yanayi na ban mamaki inda ta kwashe watanni da dama a saman Teburi kafin Manchester City ta zo ta lashe kofin.
Arteta ya bayyana cewar suna bukatar karin ‘yan wasa su hada da wadanda suke da su idan har suna bukatar lashe wani kofi mai muhimmanci.