Dan Majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Kananan hukumomin Musawa da Matazu Hon. Abdullahi Aliyu (Talban Musawa) ya yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da ya turo karin sojoji jihar Katsina domin magance matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.
Abdullahi Aliyu ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake maida martani akan wata zanga-zanga da mutanen da yake wakilta suka yi dangane da sace wasu manoma wanda ya ce karin sojoji zai taimaka matuka gaya.
Haka kuma ya cigaba da cewa shugaban kasa da duk wani mai ruwa da tsaki akan sha’anin tsaro suna da rawar da zai taka wajan magance wannan matsala da manoma ke fuskanta a wannan lokaci mai tsada
A cewar sa matakan da ake dauka akan sha’anin tsaro a yanzu ba za su wadatar ba, saboda haka yana ganin akwai bukatar a tallafi masu karamin karfi domin farfadowa da tattalin arzikin su na yau da kullum
Haka kuma ya nuna damuwarsa akan yadda mutanen kananan hukumomin Musawa da Matazu sun gagara yin barci da idanu biyu saboda wannan matsala, balantana kuma su je gonakin su da harkokin kasuwancin su na yau da kullum..
Ya kara da cewa matsalar tsaro ta zama wata babar barazana ga manoman kananan hukumomin Musawa da Matazu wanda ya ce kwana nan ya bada gudunmawar taki tirela biyu ga manoman amma matsalar tsaro ta hana su zuwa gonakin su
Kazalika Hon. Abdullahi Aliyu ya yi Allah wadai da sake bullar kashe-kashe da lalata duniyoyin jama’ar jihar Katsina musamman mutanen kananan hukumomin Musawa da kuma Matazu wanda ya ce hakan ba zai ba su damar cigaba da harkokin kasuwanci ba saboda ayyukan ‘yan ta’adda
A daidai wannan gaba na ke kara kira ga shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da cewa an zo gabar da ake da bukatar karin yawan jami’an tsaron da ke jihar Katsina domin su kawo karshen salwantar da rayukan al’umma da duniyoyin su.
“Ina san shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da ya duba wani kyakkyawan tsari akan sha’anin tsaro da zai dawo da martabar tsaron Nijeriya musamman a wannan lokaci da abubuwa suka koma baya wanda ake bukatar kawo dangantaka mai kyau tsakanin jami’an tsaro da kuma al’umma.” Inji shi
Haka kuma dan majalisar ya bayyana cewa shugaban kasa na da ikon lalubo hanyoyin daukaka darajar hukumomin tsaro ta hanyar maida hankali akan sha’anin tattalin arziki da bayar da tsari da zai kawo karshen ‘yan ta’adda da gungun barayi .
Hon. Abdullahi Aliyu ya kara da cewa yanzu haka suna yin aiki tare da dan Majalisar dattawa na shiryar Funtua da shugaban ‘yan sandan Nijeriya domin ganin an tura jami’an tsaro 600 a shiryar Funtua baki daya.
Talban na Musawa ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa wajan ganin an samu hanyar kawo karshen ta’adanci da ‘yan ta’adda da suka adabin kananan hukumomi Musawa da Matazu ganin cewa yanki da ake yin noma.