Abba Ibrahim Wada" />

Muna Bukatar Lashe Kofi A Kakar Wasan Bana Don Dawo Da Karsashi – Ronaldo

Ronaldo

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa akwai bukatar kungiyar ta lashe kofi a wannan shekarar domin a karsashin ‘yan wasa da magoya bayan kungiyar suna dusashewa.

Juventus ta samu hayewa zuwa wasan karshe na Kofin Italiya bayan da suka tashi wasa canjaras babu ci tsakaninta da abokiyar hamayyarta Inter Milan a ranar Talata, saboda nasarar da ta yi 2-1 a wasan haduwar farko a satin daya gabata.

Tawagar ta Juventus, wadda tsohon dan wasan kungiyar Andrea Pirlo yake jagoranta za ta fuskanci kungiyar kwallon kafa ta Atalanta, bayan ta doke Napoli da yammacin ranar Laraba, a haduwarsu ta farko dai sunyi canjaras babu wanda ya ci wani.

“A koda yaushe lashe kofi yana daya daga cikin abubuwan da suke daga darajar kungiya sannan kuma yana karawa ‘yan wasa da masu koyarwa da su kansu magoya baya karsashi sannan kungiyar itama zata ci gaba da kasancewa a sama-sama” in ji Ronaldo

Ya kara da cewa “Dole ne sai mun sake mayar da hankali wajen ganin mun lashe kofi a wannan kakar wasan wadda take cike da kalubale kuma a shirye muke damu tabbatar mun farantawa magoya baya rai”

Rabon Juventus da ta sha duka tun a cikin watan da ya gabata, lokacin da ta sha kashi a hannun Inter Milan da ci 2-0 a gasar Serie A, yayin da kocin kungiyar Pirlo ya ja tawagarsa a gasar ligue da na kofuna duk da ya fara jagorantar kungiyar da tangal-tangal.

Exit mobile version