Ranar 29 ga watan Mayun 2023, da aka rantsar da Asiwaju Bola Tinubu a matsayin Shugaban Nijeriya na 16, za ta ci gaba da kasancewa a cikin tarihi bisa yadda sanarwar da sabon shugaban ya yi na cire tallafin mai za ta ci gaba da kai-komo a zukatan ‘Yan Nijeriya musamman wadanda ke matukar jin radadin abin.
Duk da yake Tinubu ya yi bayanin cewa zai cire tallafin tun a lokacin da yake yakin neman zabe, amma kuma abin ya zo da ba-zata. Kasancewar man fetur ya shafi kusan dukkan bangarorin rayuwar al’umma, nan take aka fuskanci tsadar rayuwa tun daga farashin sufuri da hauhawar farashin kayan masarufi, wanda hakan ya jefa al’ummar Nijeriya cikin halin ni-‘yasu.
- Xi Jinping Ya Nanata Muhimmancin Samun Bunkasuwa Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba
- Hajjin 2023: NAHCON Ta Ware Wa Maniyyata Kwanaki 5 Don Zama A Madina
Masana harkokin da suka shafi tattalin arziki sun bayyana cewa, ya kamata a fuskanci gaskiya a kuma fahimci cewa, kasar nan na cikin wani hali na rashin kudi a kan haka ba zai yiwu a ci gaba da daukar nauyin tallafin mai ba, musamman ganin yadda kudin ya tashi daga Naira Biliyan 257 a shekarar 2006 zuwa Naira Tiriliyan 4.4 a shekarar da ta gabata.
Haka kuma ya zuwa ranar 29 ga watan Mayu, lokacin da Tinubu ya sanar da cire tallafin gaba daya, dokar alkinta albarkatun man fetur ta (PIA) ta riga ta cire tallafin kusan wata 15 da suka gabata amma gwamnatin Shugaba Buhari ta san dabarar da ta shigar da Naira Tiriliyan 3.36 cikin kasafin kudin shekarar 2022 don ta tsawaita lamarin tallafin zuwa watan Yuni na shekarar 2023.
Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta bayyana rashin jin dadinta da janye tallafin man, inda ta yi korafin cewa ya kamata gwamnati ta fadada tattaunawa da masu ruwa da tsaki tare da fito da tsare-tsaren da za su rage wa al’umma radadin da janye tallafin zai haifar a rayuwar yau da kullum, ta kuma yi barazanar tsuduma yajin aiki in har gwamnati ba ta yi abin da ya kamata ba. Amma tattaunawar da bangaren gwamnati da shugabannin kungiyar suka yi ta haifar da fahimtar juna duk kuwa da wata kotun tarayya ta haramta wa kungiyar kwadagon shiga yajin aikin, kungiyar kwadagon ta janye yajin aikin da ta shirya shiga ranar Laraba 6 ga watan Yuni tare da alkawarin za su ci gaba da tattaunawa da bangaren gwamnati don samar da mafita ga tsadar rayuwar da al’umma suka fada sakamakon cire tallafin.
Kungiykr kwadago ta bayyana cewa, cikin dalilanta na janye yajin aikin da ta shirya shiga akwai yadda suka fahimci cewa, gwamnatin tarayya ta shirya tattaunawa a kan hanyoyin saukaka wa al’umma radadin da cire tallafin man zai haifar.
Kungiyar ta kuma ce, ta lura da halin da kasa ke ciki musamman ganin ba a dade ba da kammala babban zaben kasa kuma bai kamata a tayar da hakulan al’umma ba, a kan haka suka dakatar da shirin shiga yajin aikin.
A takardar manema labarai da kungiyar ta raba wa ‘yan jarida a Abuja wanda shugaban kungiyar Joe Ajaero da sakataren kungiyar, Emmanuel Ugboaja, suka sanya wa hannu, sun bayyana cewa, sun yi bi umarnin da kotu ta bayar na su dakatar da yajin shiga aikin.
Sun kara da cewa, duk da sun amince da umarnin kotun amma suna tir da yadda ake amfani da umarnin kotu wajen danne yunkurin ma’aikata na neman hakokinsu a Nijeriya maimakon a tilasta wa gwamnati ta dauki matakin biya wa ma’aikata bukatunsu.
Cikin yarjejeniyar da aka cimma a tattaunawar da aka yi wanda shugaban ma’akata a fadar shugaban kasa, Hon. Femi Gbajabiamila ya jagoranci bangaren gwamnati sun hada har da maganar karin albashi ga ma’aikata da kuma shiri nan na karbo bashin Dala miliyan 800 don rage wa al’umma radadin da cire tallafin man zai haifar, sun bukaci a tabbatar da sanya masu karamin karfi a cikin wadanda za su amfana da tallafin.
A kan janye yajin aikin da kungiyar kwadago ta yi, majalisar wakilai ta yaba musu a kan halin dattako da suka nuna a daidai wannan lokacin, ta nemi a ci gaba da tattaunawa da bangaren gwamnati don a cimma mafita ta hanyar fahimtar juna.
Sai dai kuma, masu sana’ar hannu da injiniyoyi da sauran kananan kungiyoyi sun zargi kungiyar kwadago da sayar da hakkokin ma’aikata ta hanyar amincewa da janye yajin aiki ba tare da an biya wa ma’aikata hakokinsu ba kamar yadda ya kamata, abin da kuma shi ne makasudin shirya shiga yajin aikin.
Kungiyoyin dai sun shirya shiga gagarumin yajin aikin da ba a taba yi ba tun shekara 8 da suka wuce kafin kungiyar kwadago ta bayyana janyewa bayan da suka cimma yarjejeniya da gwamnati. Shawarar da kungiyoyin suka yi tir da ita.
Wadanda suka bayyana korafinsu sun hada da Muhammed Yunusa, mai sana’ar dinki mazaunin Kubwa, a yankin Abuja, wanda ya ce, tsadar man fetur ya sanya babu riba a harkarsu ta dinki, shi ma Olagunju Deji, mai sana’ar aski ya nemi a dawo da tallafin don su samu saukin gudanar da sana’o’insu
Duk da cewa, da farko bayan sanar da cire tallafin, an samu bayyanar layukan motoci a gidajen mai, daga baya layukan sun bace yayin da aka koma sayar da man da tsadar gaske, mafi karancin farashin shi ne inda ake sayar da lita a kan Naira 537. Wannan tashin farashin ya jefa al’umma cikin tsadar rayuwa don kusan dukkan kayan masarufi da sufuri duk sun yi tashin gwauron zabo.
Don fahimtar halin da al’umma suka shiga sakamakon cire tallafin wani mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum, Malam Bashir Dalhatu ya yi nazari da bibiyar rayuwar ‘yan uwa da abokan arziki, inda ya yi nazari halin da magidanci mai ‘ya’ya biyu ke ciki sakamakon cire tallafin man a Nijeriya.
Ya ba da misali da kudin da magidancin zai iya kashewa a abincin rana daya kamar haka: abincin safe, burodi =N600, kosai =N300, ruwan shayi ba madara= N200, ya kama= N1,100, a wata N1,100 sau 30 = N33,000. In kuma in zai yi wainar fulawa, ga yadda za ta kasance, fulawa= N400, Mai N250, Magi N100, kayan miya N50, koko N200, sukari N150, gawayi N100, ya kama: N1,250, kenan a wata, abin da za a kashe ya kama N1,250 sau 30 = N37,500 a cin abin safe kwai.
Abinci rana kuma an kiyasta zai kashe N29,100 a duk wata a abincin dare kuma zai iya kashe N21,900, in aka hada da kudin ruwan sha na N4500 duk wata zai kashe N88,500 kenan a duk wata idan zai sha shayi ba madara kuma ba zai ci abinci da kifi ko nama ba. Idan kuma wainar fulawa zai yi da safe zai kashe N93,000 a wata shi ma dai ban da kifi da nama.
Wannan lissafin na magidanci ne mai ‘ya’ya biyu kuma ba a saka kudin haya, kudin wuta, rashin lafiya, kudin zuwa aiki, omo, sabulu da sauran su.
Idan aka lura da mafi karancin albashi na N30,000 ga ma’aikatan Nijeriya wanda ma har zuwa yanzu wasu jihohi da kananan hukumomi ba su fara aiwatar da biyan albashin ba, tabbas magidanta a Nijeriya sun shiga halin matsi sosai.
Haka kuma ba a hada da kudin makarantar boko na yara, da kudin makarantar islamiyya da na kayan sawa ba wanda dukkan su cire tallafin mai ya shafe su.
Ba bangaren rayuwar daidaikun mutane ne kawai cire tallafin man ya shafa ba, har ma da ayyukan gwamnati da na manya da kananan kamfanonin domin kuwa a halin yanzu gwamnatin Jihar Kwara ta sanar da rage kwanakin zuwa aiki, daga 5 zuwa kwana 3 a mako don rage wa ma’aikata yadda suke fuskantar tsadar kudin mota. Haka kuma gwamnatin Jihar Edo ita ma ta rage kwanakin zuwa aiki daga kwanaki 5 kamar yadda aka sani zuwa kwana 2 a mako, Gwamna Godwin Obasake ya sanar da haka ta ofishinsa.
Wakilanmu sun yi mana bincike na musamman don ganin yadda tsadar rayuwa ta karu sakamakon cire tallafin mai a jihohin nasu.
Zamfara
A Jihar Zamfara, cire tallafin Mai ya tsayar da wasu ayyukan musamman na gwamnati a Gusau babban birnin Jihar Zamfara, inda ma’aikata da dama ba su iya zuwa wajen aiki, sakamakon tashin farashi man fetur da kuma karin kudin kabu-kabu da a daidaita sahu na kashi hamsin cikin dari.
Duk inda matafiya zai je an ninka kudin masu motoci ma haka, su kuma masu motoci masu zaman kansu daga ma’aikatan da ‘yan kasuwa da dama sun ajiye motocin su saboda ba su iya sayen man a farashin na naira dari biyar da hamsin.
Malam Muntaka Garba, ma’aikacin gwamnati ne, ya bayyana ra’ayinsa da cewa, “Muna fama da ciwon targade sai ga karaya, yau wata uku ba mu da albashi, muna cikin wannan jarabawar sai ga shi wadda ta fita ta same mu, don yanzu haka da yawa ma’aikata ba su iya zuwa wanjen aiki ko da kuwa a kasa ne don babu albashi, ina kwaciyar hankali yake?”.
Musa Garba, dan kasuwa wanda yanzu haka harka ta tsaya don karin farashin kayan masarufi. Ya ce hatsi ya yi tashin gwauron zabo a yanzu, duk sakamakon cire tallafin.
A nashi bangaren, Kabiru Soja, wani direba mai jigilar fasinja daga Gusau zuwa Funtuwa, ya bayyyana cewa, dole suka kara ninka kudin mota sakamakon cire wannan tallafin, duk da fasinja na wuya don jama’a sun rage tafiye-tafiye saboda rashin isassun kudi ga kuma kudin mota ya ninka.
Kano
Tun bayan bayyana cire tallafin man fetur da shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ayyana, jama’a a Jihar Kano suka tsinci kansu a wani hali da ba a taba zatonsa ba a karkashin gwamnatin demokaradiya, gwamnatin da al’umma suka zaba bisa kyautata zaton za ta yi masu adalci wajen samar masu da sauki a cikin harkokin yau da kullum.
Kasancewar Kano a matsayin jihar da ta jima tana rike da kambun cibiyar ciniki mai tarihin karbar baki daga koina cikin kasar nan da ma sauran kasashen duniya, wanda hakan tasa ake amfani da ababan hawa masu amfani da man fetur masu yawan gaske, yanzu sai gashi bayyana cire wannan tallafi ya jefa dubun-dubatar jama’a cikin tsaka mai wuya wanda hakan ya tilasta wa wasu magidanta zabar ajiye ababen hawansu tare da takawa da kafa zuwa wuraren harkokinsu na yau da kullum, musamman ‘yan kasuwa da ma’aikatan gwamnati.
Lamarin ya fi kamari da ban tausayi da safe lokacin da dalibai ke kokarin tafiya makarantunsu, wuraren da ake biyan Naira hamsin ya koma 150, sannan kuma ga karancin ababen hawan domin wasu masu sana’ar sun zabi ajiye baburansu masu kafa uku gudun samun matsala da kwastomi sanadiyyar tashin farashin sufuri. Haka al’amarin yake ga jama’ar da ke kan hanyar zuwa wasu wurare da mata masu bukatar zuwa asibiti, za ka ga mace da tsohon ciki tana tattaki da kyar sakamakon tsadar farashin abin hawa wanda kusan na neman fin karfin jama’a.
Sakamakon wannan tsada ta man fetur wasu magidantan, dole ta sa sun sauya salon harkokin gudanar da al’amuran gidajensu ta hanyar rage yawan bukatu domin tafiya daidai da halin da ake ciki. Haka nan an fara samun raguwar zumuncin mata masu akidar zirga-zirgar zuwa gidajen bukukuwa ba gaira ba dalili, haka su ma masu yawon bude ido sun fara zama a unguwanninsu, kasancewar kudin hayar ababen hawa nan ema ya gagari kundila.
Yobe
Ta la’akari da yanayin matsin rayuwar da matsalar tsaron Boko Haram ta jefa miliyoyi a yankin gabashin Nijeriya; inda daruruwa suka mutu, tare da asarar biliyoyin naira, kana da halin da ambaliyar ruwa suka jefa musamman jihar Yobe, ana hasashen cire tallafin man fetur wanda gwamnatin tarayya ta ayyana makon da ya gabata zai yi mummunan illa ga al’ummar jihar Yobe.
Yobe jiha ce wadda al’ummarta suka dogara da noman damina da na rani, kasuwannin kauye da sauran harkokin da suka rataya da man fetur, wanda cire tallafin zai rubanya farashin man, al’amarin da zai jawo tashin farashin kayan abinci da na masarufi, wanda ko shakka babu zai jefa rayuwa talaka cikin mawuyacin hali.
Kimanin kaso 70 cikin 100 na al’ummar jihar Yobe sun dogara ne walau noman rani (kayan lambu da shinkafar kadada) ko na damina, kiwo da cin kasuwannin kauye, wanda janye tallafin zai shafi harkokin noman kai-tsaye, inda zai yi wahala manoma su jure sayen litar man fetur daya kan N540 (farashin gwamnati) a gonakin noman rani, karin kudin mota wanda ya ribanya tare da na sauran kayan masarufi.
Matakin ya janyo fargaba ga manoman damina, sakamakon irin yadda zai shafi zirga-zirgar yau da kullum kan ababen hawa zuwa gonaki, sannan da bangaren ‘yan kasuwa, masu cin kasuwannin kauye, na mako-mako da makamantansu, wanda kafin janye tallafin, kananan ‘yan kasuwar sun koka dangane da koma baya da ake fuskanta a fannin kasuwancinsu, “nawa za ka biya kudin mota zuwa kasuwa, a karshe sai ka dawo gida babu ko kwabo.” Ta bakin wani dan kasuwa.
Rikicin Boko Haram a jihar Yobe ya shafi miliyoyin jama’a kai-tsaye da a kaikaice, wanda ya jawo asarar dimbin rayukan jama’a, barnata dukiyoyin da Allah ne kadai ya san yawansu, raunata harkokin kasuwanci da na tattalin arzikin dubban jama’a, wanda har yanzu matsalar ba ta kau ba a zukatan ‘yan jihar Yobe.
A shekarar da ta gabata, ambaliyar ruwa ta mamaye yunkurin al’ummar jihar na farfadowa daga ta’addancin Boko Haram, ibtila’in da ya mayar da hannun agogo baya, inda ya barnata amfanin gona, rusa dubban gidaje tare da shafe wasu kauyuka a jihar. Wani babban abin damuwa shi ne, gwamnatin tarayya ba ta dauki wani matakin a zo a gani ba wajen tallafa wa jama’a, face na janye tallafin man fetur.
Kamar yadda kididdigar masana ta tabbatar, sama da kaso 70 cikin 100 na al’ummar jihar Yobe sun dogara ne kan harkokin noma, kiwo da cin kasuwannin kauye, a haka al’ummar jihar suke rayuwa ba tare da wani tallafin gwamnatin jihar ba, balle na tarayya wanda hakan ya kara tsananin yanayin rayuwa.
Nasarawa
Tun bayan da sabon Shugaban Nijeriya ya bayyana cire tallafin man fetur, gidajen mai a Jihar Nasarawa suka juya litar mai zuwa farashi mai tsada.
Wannan janye tallafin ya janyo wahalhalu ta kowani bangare. Masu ababen hawa na kasuwanci sun kara farashi ninki biyu. Wasu masu ababen hawa da ke zuwa wuraren bukatunsu na yau da kullun sun jingine ababen hawan sun gwammace takawa a kasa ko hawa na kasuwa.
Kayayakin masarufi tuni sun yi tashin gwauron zabo. Kayayakin abinci su ma suna kara farashi. Gidajen mai babu layi amma masu saya sun ragu, sakamakon tsadar man.
Wahalar ta shafi masu ababen hawa da masu hawa da ‘yan kasuwa.
A Babbar Tashar mota ta Yahaya Sabo inda nan ne aka fi gudanar da hada-hadar sufuri, an kara kashi 30% na farashin mota.
A kasuwar shinkafa da ke cikin Lafiya, an kara farashi sakamakon karin kudin mota. Jama’a da dama suna takawa a kasa zuwa wasu wuraren da babu tazara sosai.
Kebbi
A Jihar Kebbi kuwa, farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabo a sakamakon janye tallafin mai, inda ya karu zuwa Naira 520 da kuma Naira 545 a kowace lita a gidajen mai da dama da kuma sama da Naira 800 a kasuwar bayan fage.
Sakamakon karancin kudin safara zuwa wurare daban-daban, a ciki da wajen jihar an kara kudin sufuri. Masu tuka babura na kasuwanci da ke karbar Naira 100, N1,50 zuwa wurare daban-daban yanzu haka suna karbar Naira 250, N300 yayin da daga Birnin Kebbi zuwa Kalgo, Jega ta motocin kasuwanci da ake shiga a kan N200, N300 yanzu N400, N700. Haka Kuma zuwa Ilorin, Legas. Yanzu N15,000/N17000 sabanin N12,000/15,000, yayin da Abuja daga Kebbi yanzu ya koma N13,000 sabanin N10,000.
A yayin da yake magana kan wannan matsala da ta kunno kai, wani direban babur da ke zirga-zirga daga garin Kalgo zuwa Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi, Umar Awwal, ya shaida wa wakilinmu cewa, ba su da wani zabi da ya wuce su kara kudin babur saboda suna sayen man kan kudi N550 a gidajen mai yayin da a kasuwar bayan fage kuma, ake sayar da shi kan Naira 750, ko kuma N,800 a kowace lita.
“Wannan wani lokaci ne mai wahala ga dukkanmu, za mu shawo kan lamarin kamar yadda muka tsira a lokacin siyasar rashin kudi a zamanin Baba Buhari,” in ji shi.
Wani manomin rani Faruk Muhammad Koko, ya bayyana cewa manoma da yawa ba za su iya shiga noman rani na bana ba saboda farashin mai ya wuce kima, domin “muna sayen dan kadan ne a kan kudi Naira 194 a matsayin farashi gwamnati. Haka kuma a kasuwar bayan fage Naira 210 ko 240 ne kuma a wancan lokacin har yanzu muna ganin farashin ya yi tsada, amma abin takaici matuka bayan rantsar da Bola Ahmed Tinubu sai kawai muka ji sanarwar cire tallafin man fetur, da me za mu ji?” Koko ya koka.
Ya kara da cewa yadda al’amura ke tafiya a kasar nan, idan aka ci gaba da yiwuwar samar da abinci a kasar zai ragu matuka kuma yunwa da wadata da rashin tsaro za su karu. “Domin da yawa daga cikin mutanenmu za su rasa sana’o’insu da ayyukansu da suke yi a kowace rana wanda sakamakon cire tallafin man fetur.” In ji shi.
Yanzu dai kallo ya koma kan Gwamnatin Tarayya da Kungiyoyin Kwadago na NLC da TUC wadanda suka cimma matsaya a kan ci gaba da tattaunawa game da hanyoyin da za a bi a rage wa ‘Yan Nijeriya radadin da cire tallafin man ya sabbaba.
Kamar yadda rahotanni suka nuna, gwamnatin ta yi alkawarin bullo da wasu tsare-tsare da za su saukaka yanayin rayuwar da ake ciki a kasar, inda a bangaren ‘yan kwadagon suke neman a kara yawan albashi mafi karaci ya koma daga Naira 30,000 zuwa 200,000 da sauran wasu matakai da za su kyautata yanayin ma’aikata. Abin da ya rage yanzu shi ne, ko gwamnatin za ta girmama yarjejeniyar da za a kulla sakamakon janye yajin aikin ko kuma abin zai zama kamar cin kwan makauniya kamar yadda aka saba gani a lokutan baya? Lokaci ne kadai zai tabbatar musamman bisa yadda masana da dama suke ta sharhi kan tataburzar da aka yi a tsakanin ‘yan kwadagon da gwamnati.