• English
  • Business News
Sunday, October 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Muna Fata Masu Talla A Kafafen Sada Zumunta Su Fadakar Kan Shirye-shiryen Tinubu Na Habaka Tattalin Arziki 

by Sulaiman
2 years ago
in Labarai
0
Yajin aiki
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga ƙungiyar masu saka tallace-tallace a kafafen yaɗa labarai da sada zumunta su mayar da hankali wajen faɗakar da ‘yan Nijeriya kan sababbin tsare-tsaren tattalin arziki waɗanda gwamnatin Tinubu ta zo da su, waɗanda burinsu shi ne haifar da cigaban ƙasa ta fuskar tattalin arziki.

Idris ya yi kiran ne a ranar Alhamis a Abuja a lokacin buɗe babban Taron Masu Tallace-tallace na Ƙasa mai taken “Sadarwar Talla a Matsayin Mai Kawo Nagartaccen Sauyi Ga Ƙasa”.

  • Yadda Kasar Sin Ke Ba Da Gudummawar Tinkarar Sauyin Yanayi A Duniya
  • Sojojin Somaliya Sun Kashe Mayakan Al-Shabab 60 A Yankin Tsakiyar Kasar

A cewar hadimin musamman na ministan kan yaɗa labarai, Malam Rabi’u Ibrahim a wata sanarwa da ya fitar, inda yace, ministan ya samu wakilcin Darakta-Janar na Hukumar Wayar Da Kai ta Ƙasa (NOA), Mista Lanre Issa-Onilu, ya yi la’akari da muhimmiyar rawar da ƙwararrun masu sana’ar tallace-tallace a kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen yaɗa labaran da za su yi tasiri a wajen jama’a.

Ya ce su na kan cikakken matsayin da za su iya jan akalar samun sauyi a tsarin tattalin arziki da zamantakewar Nijeriya ta hanyar yi wa jama’a yekuwar yadda za su ci moriyar sababbin tsare-tsaren da gwamnatin ke aiwatarwa.

Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin tallafa wa ƙananan sana’o’i, da Shirin Shugaban Ƙasa na Bada Rance Bisa Ƙa’idoji da shirye-shiryen rage raɗaɗin rayuwa, waɗanda aka yi domin ‘yan kasuwa, masu aikatau, masu sufuri, ‘yan talla, da masu ayyukan fasaha da bada ƙananan rance.

Labarai Masu Nasaba

Nijeriya Ta Zamo Ƙasa Mafi Ƙarancin Tsammanin Tsawon Rayuwa A Duniya

NUJ Ta Yi Maraba Da Sakin Ƴan Jaridar Da DSS Ta Kama A Jana’izar Mahaifiyar Shugaban APC

“Sana’o’i mafi ƙanƙanta a ƙasar nan su miliyan 1 za su ci moriyar rancen kuɗi N50,000 kowannen su, yayin da manyan sana’o’i za su ci moriyar rance daga Asusun Naira Biliyan 75 da aka tanadar.”

Ministan ya ƙara da cewa waɗannan shirye-shiryen ɗori ne a kan waɗanda da ma can an bayyana su kuma ana aiwatar da su, misali samar da motocin safa-safa masu aiki da hasken rana da gwamnatocin jihohi za su ƙaddamar, domin rage wahalar da cire tallafin man fetur ya janyo.

Ya ce duk waɗannan tsare-tsaren ba wai an yi su da ka ba ne, a’a, sai da aka tsara su a tsanake cikin Ajandar Sabuwar Fata ta Shugaban Ƙasa, wadda ta haɗa da sauya fasalin tattalin arziki don a samar da cigaba mai ɗorewa; ƙarfafa tsarin tsaro don samar da kwanciyar hankali da arziki; haɓaka aikin gona don wadata ƙasa da abinci; buɗe hanyoyin makamashi da ma’adinai don samun cigaba mai ɗorewa da kuma bunƙasa hanyoyi da gine-gine a matsayin su na turakun kawo cigaba.

Sauran su ne: bada muhimmanci ga harkokin ilimi, kiwon lafiya, da taimakon jama’a a matsayin muhimman ginshiƙan cigaban ƙasa da gaggauta faɗaɗar hanyoyin tattalin arziki ta hanyar masana’antu, aiki da komfuta, fasahohin zamani, ƙere-ƙere, da ƙirƙire-ƙirƙire.

Ministan ya ce wannan gwamnatin ta sadaukar da kan ta ne ga samar da bayanai a kan lokaci kuma ta nagartacciyar hanya, kuma ya bada tabbacin cewa zai gudanar da aikin da aka ɗora masa a buɗe kuma a mutunce.

Ya ce: “A yayin da mu ke bada bayani ba tare da ɓoye komai ba kuma a cikin nagarta, ina kira a gare ku a matsayin ku na ƙwararru da ku tattaro ƙwan ku da kwarkwatar ku ku taimaka mana domin mu isar da bayani dalla-dalla ga jama’a ba tare da wata hargowa ko sauya shi ba.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AmurkaMinista
ShareTweetSendShare
Previous Post

Nijeriya Ta Koma Ta 44 A Fagen Kwallon Kafa A Duniya

Next Post

Sana’ar Kitso Ta Yi Min Komai – Safiya Yakubu

Related

Nijeriya Ta Zamo Ƙasa Mafi Ƙarancin Tsammanin Tsawon Rayuwa A Duniya
Labarai

Nijeriya Ta Zamo Ƙasa Mafi Ƙarancin Tsammanin Tsawon Rayuwa A Duniya

45 minutes ago
NUJ Ta Yi Maraba Da Sakin Ƴan Jaridar Da DSS Ta Kama A Jana’izar Mahaifiyar Shugaban APC
Labarai

NUJ Ta Yi Maraba Da Sakin Ƴan Jaridar Da DSS Ta Kama A Jana’izar Mahaifiyar Shugaban APC

2 hours ago
Ranar Malamai ta Duniya: Ƙungiyar NUT Ta Koka Kan Ƙarancin Malamai 194,000 A Nijeriya
Labarai

Ranar Malamai ta Duniya: Ƙungiyar NUT Ta Koka Kan Ƙarancin Malamai 194,000 A Nijeriya

5 hours ago
Sanata Ndume Ya Yaba Wa Gwamna Zulum Kan Shirinsa Na Tura Sojoji Kirawa
Labarai

Sanata Ndume Ya Yaba Wa Gwamna Zulum Kan Shirinsa Na Tura Sojoji Kirawa

6 hours ago
Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Alhinin Rasuwar Dattijo, Ambasada Jabbi Maradun
Labarai

Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Alhinin Rasuwar Dattijo, Ambasada Jabbi Maradun

7 hours ago
Ban Bar PDP Ba, Ina Gangamin Hadin Gwiwa Ne Don Tunkarar APC A 2027 – Atiku
Labarai

Atiku Ya Zargi Tinubu Da Fifita Ziyarar Siyasa A Maimaikon Ta Waɗanda Rashin Tsaro Ya Shafa 

8 hours ago
Next Post
Sana’ar Kitso Ta Yi Min Komai – Safiya Yakubu

Sana'ar Kitso Ta Yi Min Komai - Safiya Yakubu

LABARAI MASU NASABA

CMG Zai Watsa Shirin Nishadantarwa Na Murnar Bikin Zhongqiu Gobe Da Dare

CMG Zai Watsa Shirin Nishadantarwa Na Murnar Bikin Zhongqiu Gobe Da Dare

October 5, 2025
Nijeriya Ta Zamo Ƙasa Mafi Ƙarancin Tsammanin Tsawon Rayuwa A Duniya

Nijeriya Ta Zamo Ƙasa Mafi Ƙarancin Tsammanin Tsawon Rayuwa A Duniya

October 5, 2025
Yawan Mutanen Da Suka Yi Zirga-zirga A Rabin Farkon Hutun Bikin Kafuwar PRC Da Bikin Zhongqiu Ya Kai Biliyan 1 Da Miliyan 243

Yawan Mutanen Da Suka Yi Zirga-zirga A Rabin Farkon Hutun Bikin Kafuwar PRC Da Bikin Zhongqiu Ya Kai Biliyan 1 Da Miliyan 243

October 5, 2025
NUJ Ta Yi Maraba Da Sakin Ƴan Jaridar Da DSS Ta Kama A Jana’izar Mahaifiyar Shugaban APC

NUJ Ta Yi Maraba Da Sakin Ƴan Jaridar Da DSS Ta Kama A Jana’izar Mahaifiyar Shugaban APC

October 5, 2025
Kamfanin Sin Ya Kaddamar Da Ginin Katafaren Wurin Shakatawa Na Zamani A Ghana

Kamfanin Sin Ya Kaddamar Da Ginin Katafaren Wurin Shakatawa Na Zamani A Ghana

October 5, 2025
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, Ta Nuna Damuwa Kan Ƙarancin Malamai A Duniya

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, Ta Nuna Damuwa Kan Ƙarancin Malamai A Duniya

October 5, 2025
Za A Gudanar Da Taron Motoci Masu Amfani Da Fasahohin Zamani Na Duniya Na Shekarar 2025 A Beijing

Za A Gudanar Da Taron Motoci Masu Amfani Da Fasahohin Zamani Na Duniya Na Shekarar 2025 A Beijing

October 5, 2025
Ministan Harkokin Wajen Sin Zai Ziyarci Italiya Da Switzerland

Ministan Harkokin Wajen Sin Zai Ziyarci Italiya Da Switzerland

October 5, 2025
Ranar Malamai ta Duniya: Ƙungiyar NUT Ta Koka Kan Ƙarancin Malamai 194,000 A Nijeriya

Ranar Malamai ta Duniya: Ƙungiyar NUT Ta Koka Kan Ƙarancin Malamai 194,000 A Nijeriya

October 5, 2025
Sanata Ndume Ya Yaba Wa Gwamna Zulum Kan Shirinsa Na Tura Sojoji Kirawa

Sanata Ndume Ya Yaba Wa Gwamna Zulum Kan Shirinsa Na Tura Sojoji Kirawa

October 5, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.