Ma’aikatar tsaron Nijeriya, ta yi gargadi da kakkausar murya ga wadanda ke yin kira ga sojoji da su yi juyin mulki.
Ma’aikatar ta ce hakan babban laifi ne na cin amanar kasa, kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanadar.
- Xi Ya Tafi Halartar Taron Kolin BRICS Karo Na 16 A Rasha
- Paul Biya Ya Koma Kamaru Bayan Rade-radin Mutuwarsa
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na shelkwatar tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau, ta bayyana. ewa rundunar sojin Nijeriya ta mayar da hankali ne ga ainihin aikin da kundin tsarin mulkin ya gindaya mata.
Gusau ya ce kwarya-kwaryar zaman lafiya da aka samu a kasar ta tabbata ne sakamakon gudunmawa da goyon bayan da shugaba Tinubu ya ke bai wa rundunar sojin.
Ya kuma tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa rundunar sojin, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro za su dauki matakan da su ka dace wajen kawar da duk wani yunkuri na yi wa kundin tsarin mulki karan-tsaye.
Sanarwar na zuwa ne yayin da ake bayyana damuwa game da wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta na wani gungun mutane da ke yi wa sojoji magiya kan su yi juyin mulki.
Wannan ba shi ne karon farko da ake samun masu irin wannan kiraye-kiraye ba, na sojoji da su yi juyin mulki a kasar.