Kungiyar kwallon kafa ta Serie A, Juventus, ta sanar da dawowar Paul Pogba daga Manchester United.
Juve ta bayyana hakan ne a shafinta na yanar gizo, inda ta kara da cewa “Lokacin da muka yi bankwana da tauraron dan Wasan mu, koyaushe muna kwana da kyakkyawan fata cewa, wata rana za mu sake ganin juna, ba dade ko ba jima. Abin da ya faru ke nan da Pogba.”
Kulob din na Italiya ya kara da cewa, “Paul Pogba ya dawo Turin. Ya bar mu yana da kuruciya ya dawo mana cikakken mutum kuma zakara, amma akwai abu daya da bai canza ba – sha’awar sake rubuta shafukan tarihin kulob din na samun nasarori da ba za mu manta ba tare. Pogba ya dawo kuma muna maraba da shi sosai cikin farin ciki. ”
Pogba ya lashe kofunan Seria A guda hudu a farkon zamansa a Juve, inda ya zura kwallaye 34 a wasanni 177 da ya buga a dukkanin gasa kafin ya koma Man United kan kudi fam miliyan 89 da yafi Kowanne tsada a tarihi a shekarar 2016.