Amurka ta ce tana da masaniya a kan rahotannin tsare dan kasarta ma’aikacin Binance da hukumomin Nijeriya suka yi.
A watan da ya gabata ne aka kama shugaban kamfanin Binance, Tigran Gambaryan tare da abokin aikinsa, Nadeem Anjarwalla, wanda ke da fasfon Birtaniya da Kenya a wani bangare na binciken kaucewa biyan haraji da gwamnatin Nijeriya ke yi wa kamfanin kirifto din.
- Gwamnan Zamfara Ya Yi Kira A Kara Yawan Sojoji A Jihar Don Yaki Da ‘Yan Bindiga
- HOTUNA: Yadda Jami’an Tsaro Suka Lalata Haramtacciyar Matatar Danyen Mai A Ribas
Mai magana da yawun ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya, ya shaida wa BBC cewa, “A duk lokacin da aka samu wata matsala ta tsare dan kasarsu a wata kasa, to ofishin jakadancin da ke kasar na yin duk mai yiwuwa wajen bayar da taimakon da ya dace.”
Ofishin jakadancin ya ki bayar da cikakken bayanai game da tsare dan kasar tasu, yana mai cewa saboda dalilai na sirri.
Yanzu haka Nadeem Anjarwalla, ya tsere daga hannun hukumomin tsaro a Nijeriya.
Mahukuntan Nijeriya dai sun ce suna aiki da jami’an tsaron kasa da kasa don samar da takardar sammaci sake kama Mista Anjarwalla.