Fitacciyar ‘yar siyasa kuma mai fafutukar sama wa mata ‘yanci a harkokin siyasar Nijeriya, HAJIYA HALIMATUS SA’ADIYYA HUSSAINI SHELLENG, ta nuna kwarin gwiwarta a kan gyaruwan harkokin siyasa wadda ta ce saboda tunanin gaba za ta yi kyau ya sa suka tsunduma a siyasa.
Haka nan ta tabo batutuwa da dama da suka shafi mata a harkokin siyasa, musamman ta anuna rashin gamsuwarta game da kin ba da dama ga mata su fito takara lokacin zaben fid da gwani da jam’iyyu da aka kammala kwanan baya. Ga cikakkiyar tattaunawarta da wakilinmu na Jihar Adamawa, MUH’D SHAFI’U SALEH:
Da yake a ‘yan kwanakin nan ne jam’iyyun siyasa suka gudanar da zaben fid da gwani, kun gamsu da kamun ludayin jam’iyyun ta fuskar shigo da mata takara a matakai daban-daban?
Gaskiya wasu jam’iyyu ba su kyauta wa mata ba, saboda an sauke mata da dama daga mukamai daban-daban, kama daga majalisar dokokin jihohi da majalisun tarayya na kasa, an sassauke mata masu yawa, amma ba mu da ja kuma mun hakura mun yarda da yin Allah.
Jam’iyyun da suka bai wa mata damar kun gamsu da irin damar da suka bayar din?
Toh, a gaskiya wasu wuraren za mu iya gamsuwa da su, saboda a cikin matan ma mun san masu cin zabe, kuma mun san wadanda ba za su iya cin zabe ba, amma wasu wuraren kuma gaskiya ba mu gamsu ba, amma dai duk da haka mun yi hakuri tun da babu yadda muka iya, mun yi mubayi’a.
Kamar ke kin nemi ki tsaya takaran ne ba ki samu ba, ko kin samu?
A’a, tun da na fara siyasana tsawon shekaru 11, ban taba tunanin zan yi takara ba, kuma ma ban taba kwadayin zan yi takara ba.
Me ya sa ki sha’awar tsayawa takara ba?
Haka nan kawai, domin ni mai bankasa siyasa ce tun daga tushe, idan zan yi takara, ka ga ba zan bai wa duk wanda yake son samun wani matsayi ba dama kenan, dole ne zan zauna a wuri guda kuma ba zan iya cimma burina ba.
Ba ki ganin irin wanann tunani ne ke hana jam’iyyun ba ku damar tsayawa takara?
A’a, ra’ayina ne haka, amma ba kawai ina shakkan kaina ba ne, koma wani irin fom na saya na yi imani da Allah na yarda da kaina zanci zabe, amma kawai ra’ayi ne irin nawa wanda ban son in yi takara a matsayina na ‘yar gwagwarmayar kwato wa mata ‘yanci.
Ba wai don ni ba zan yi takara ba shi ya sa aka hana wasu, a’a, wasu mun yarda ba za su ci zabe ba, amma duk da haka ba za a hadu a zama daya ba, akwai masu iya cin zaben, amma an sassauke kuma ma wasu kuma ba a dai bari yawanci matan sun shiga zabe ba gaskiya.
Ana ganin Jihar Adamawa ta kafa tarihi ta hanyar tsayar da mace a matsayar ‘yar takarar kujerar gwamna, a matsayinki na mace ya kika ji da hakan?
Gaskiya ni na fi kowa farin ciki, duk da dai ba jam’iyyana take ba, amma na fi kowa farin ciki saboda gwagwarmayar da na yi ta yi a baya wajen mata su samu shiga harkokin siyasa. Na yi fushi a baya lokacin da mata ba su samu shiga ba a duk jam’iyyun ba ma jam’iyya guda daya ba, saboda duk gwagwarmayar da nake yi bai tsaya ga jam’iyya guda ba, saboda ina yi ne domin mata gaba daya su sami dama ko ba wacce take jam’iyyana ba, duk za mu hadu mu mata murna tare da fatan alheri, amma ba wai don ina taya ta murna shi ne zan bar jam’iyyar da nake in koma wurinta ba.
Ba za ki yi fatan ganin mace ta zama gwamna kuma a lokacin guda ku ne kwamishinoni, sakatarorin gwamnati da sauran mukamai, ko dai ke ba haka za a yi ba?
Toh, gaskiya ina ganin ni na ma fita farin ciki, batun ta kafa mulki kuma wannan na Allah ne ba zan ce komai a kai ba, idan ta ci zabe rabonta ne, amma mu ba za mu bar inda muke ba, saboda mu ba za mu zama masu ci su lashe baki ba.
Ganin ita kanta jam’iyyar PDP ta bai wa mata dama, wasu dama ‘yan majalisa ne, ta kuma sake ba su daman takara, kina ganin kwalliya ta biya kudin sabulu?
Gaskiya kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, wacce aka bai wa ta sake takara mace daya ce, ita kuma da babu duk daya ce a wurinmu, saboda ba ta amfanar da mata ko kadan, mu da ba ita aka bai wa ba, domin da a ba ta wannan takara gwanda a bai wa namiji musan ba mace ba ne a wurin, amma gaskiya kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Wannan ya sa wasu ka iya ganin kamar kuna kwance wa kanku zani a kasuwa ne?
Ba kwance wa juna zani muke yi a kasuwa ba, muna fadin gaskiya ne, saboda mu damuwarmu matan ne su amfana, kuma mun goyi bayanta a baya har ta ci zabe, domin muna ganin za ta amfanar da mata, amma ko a yankinta babu abin da ta yi, saboda na samu korafi a yankinta daga wurin mata sama da 70, wadanda su ba sa ko samun ganinta ballantana ta taimaka musu. A
mata gwagware da su da ‘ya’yansu suna gida, wani wurin ma makarantu sun lalace ta kasa gyara musu har ma akwai wuraren da babu makarantun kuma ba ta iya rubuta wa ta ce babu makaranta ba, to ka ga da ita da namiji duk daya ne a wurinmu domin ba mu amfana da ita ba.
Ba ki taba rike wani mukami na gwamnati ba, kuma jama’a sun yarda da ke, sun amince miki, ta yaya kika samu damar mallakar jama’arki haka?
Ni dama mai son jama’a ce, da siyasa da babu siyasa na rike su gaskiya, cikinsu akwai wadanda na yi wa aure, akwai wadanda na biya kudin karatunsu, na bai wa wasu jari, wasu cinsu da shan wasunsu, magani duk ni nake musu, ganin haka su kuma suka yarda da Allah suka yarda da ni, sun amince wa kansu ba zan taba cutar da su ba, shi ya sa duk inda na ce ko na ja musu layi ba za su tsallake ba. Haka kuma idan dama ta zo mana, muna taimaka musu da ita.
Hajiya kamar a ina kike samun kudaden gudanarwa, ganin ke ba wani mukami kike rike da shi ba?
Ka san duk abu idan za ka yi shi da zuciya daya, sai Allah ya taimaka maka, kuma siyasa da ma ba wai na dauke ta hanyar cin abincina ba ne, akwai dan abubuwan da mutum yake yi a gefe, siyasa muna yin ta ne bisa tsammanin gaba za ta yi kyau, amma ba mun dauke ta hanyar gudanar da rayuwarmu ba ce.
Kina da sha’awar neman wani mukamin siyasa a nan gaba?
Wannan abu ne wanda Allah ya bai wa kansa sani, ba za mu iya fadar sa ba, amma dai a yanzu haka muna musu saboda Allah ne, kuma su ma suna yi mana abin da muke so, ni a yanzu haka ban san ko zan nemi wani abu a gaba ba, amma sai idan gaban ya zo.
Idan da za su nemi ki wakilce su za ki amsa kiransu?
Wannan kuma wani abu ne na daban, ga Wazirin Adamawa jama’a sun neme shi kuma ya fito, kuma ya samu karbuwa, idan jama’a suka nemi hakan, za mu iya amsa kiran su domin mutane rahma ne.
Alhaji Atiku Abubakar ya samu tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ku mata yaya kuka ji da samun tikitin?
Ai mu ba mu da abin da za mu ce masa sai addu’ar Allah ya tabbatar da mulkinsa, saboda shi ya taimaka wa mata, babu abin da za mu ce masa sai dai fatan Allah ya kai mu lokaci da za mu biya shi da kuri’ummu.