Shugaban kamfanin mai na kasa (NNPCL) Mele Kyari, ya bayyana cewa coci-coci da masallatai da jami’an tsaro da kuma al’ummomin da bututun mai ya bi ta yankinsu, duk suna da hannu wajen fasa bututun mai domin sacewa.
Ya ce: “Kamar yadda ku ma kun sani, akwai munanan ayyukan masu fasa manyan bututun mu tun daga Atlas Cobe har zuwa Ibadan, sannan da kuma duk wasu dakunan ajiya (Depot) guda 37 da muke da su a fadin kasar nan.
- Jami’an KAROTA Sun Cafke Tirela Makare Da Giya A Kano
- Sin Ta Yi Watsi Da Rahoton MDD Game Da Batun Kare Hakkin Bil Adama A Xinjiang
Dukkansu babu wanda za a iya tura mai ta cikinsa ayau. “Kuma kowa ya san me ya sa ba ma turawa, yau shekara 15 kenan, Bututunmu na Warri zuwa Benin ba mu yi amfani da shi ba.
Kowanne digon Mai daya muka tura sai ya bace. Kuma ba shakka, za ku tuna abin bakin ciki da lamarin gobara ya afku a kusa da Warri, kusa da Sapele wanda ya kashe mutane da dama.
“Akwanakin baya, a wani yanki a Legas, Lokacin da gobara ta tashi a daya daga cikin bututunmu, mun gano cewa ana satar man daga cikin gidaje da Masallatai da Coci-coci.
“Hakan yana nufin kowa yana sane da satar man. Babu yadda za a yi a kwashi mai cikin Tanka a cikin unguwannin Jama’a amma ace ba a gani ba.”
Sai dai kuma, da suke mayar da martani kan zargin na shugaban NNPC, wasu malaman addinin Kirista sun kalubalance shi da ya fallasa wuraren ibadar da ake zargi da satar man.
Tsohon Daraktan Harkokin Shari’a na Kungiyar Kiristoci ta Kasa, Ebangelist Kwakur ya musanta lamarin tare da bayyana cewa, “Ba na tunanin yana da wata kwakkwarar shaida a kan haka.
Idan kuma yana da ita ya fallasa kowa ya gani. Akwai yiwuwar za a iya samun wani gari da ake da masallaci da coci kuma a samu barayi a cikinsa.
Kuma mu a matsayinmu na shugabannin addini ba za mu iya daukar nauyin laifukan da daidakun jama’a ke yi ba.”
Haka shi ma a martaninsa, Babban Limamin Masallacin Al-Habibiyya da ke Abuja, Imam Fuad Adeyemi ya bukaci gwamnati ta hukunta duk wani malamin da aka samu yana da hannu a kan badakalar ta satar mai.
Ya ce ya amince da batun na Kyari cewa akwai wasu coci-coci da masallatai da suke taimakon cin hanci da rashawa saboda limamansu suna kasuwanci ne da addini.
Hakazalika, Mele Kyari ya bayyana cewa Nijeriya za ta dakatar da sayo man fetur daga kasashen waje daga tsakiyar badi idan Allah ya kai mu.
Kyari ya bayyana haka ne a ranar Talata, yayin gudanar da taron manema labarai na ma’aikatu da ake yi mako-mako wanda kwamitin yada labarai na fadar shugaban kasa ke shiryawa a fadar shugaban kasa. Ya nunar da cewa man da za a rika tacewa daga matatar mai ta Dangote da sauran matatun main a gwamnati da kananan da ake da sun a ‘yan kasuwa zai kawo kawo karshen sayo man daga waje har ma kasar ta fara fitarwa ita ma.
Ya ce sabo karuwar yawan ‘Yan Nijeriya masu matsakaitan karfi, adadin man da ake da amfani da shi ya karu ainun amma duk da haka za a samu wadatar man da ake sarrafawa a cikin gida har ma a rika fitarwa zuwa waje.