A baya bayan nan, wasu ’yan siyasar Amurka sun sake bullo da zarge zarge marasa asali kan kasar Sin, suna masu bayyana Sin din a matsayin mai tallafawa masana’antun kera makamai na kasar Rasha, har ma suna kira da a kara kakkabawa wasu sassa, da daidaikun jama’ar Sin takunkumai ba gaira ba dalili. A daya bangaren kuma, kungiyar tsaro ta NATO, bisa jagorancin Amurka ita ma ta zargi Sin da ingiza rikicin kasar Ukraine.
Ta hanyar shafawa kasar Sin kashin kaji don gane da rikicin na Ukraine, Amurka da NATO suna kokarin saukewa kan su alhakin ci gaba da rura wutar tashin hankalin da ya ki ci ya ki cinyewa, tare da nunawa sassan kasa da kasa su ne masu son wanzar da zaman lafiya da lumana.
- Sin Ta Kashe Yuan Biliyan 300 A Aikin Gina Tituna A Xizang A Tsakanin Shekarar 1953-2023
- Wakilin Sin: Dage Takunkumin Hana Shigo Da Makamai Zai Taimakawa Gwamnatocin Afirka Ta Tsakiya Wajen Kara Karfin Tsaro
To sai dai kuma, magana ta gaskiya ita ce Amurka da kungiyar NATO, na so ne su haifar da wani yanayi da zai sa a rika ganin baiken kyakkyawar dangantakar raya tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Rasha, ta hanyar kitsa karairayi, cewa wai Sin na samarwa Rasha tallafin harkokin soji, duk da cewa ba su nuna wasu hujjoji na zahiri da za su tabbatar da zargi nasu ba.
Wasu alkaluma ma sun tabbatar da cewa, kaso sama da 60 bisa dari na kayayyakin ayyukan soji, da na ayyukan soji da farar hula da Rasha ke saya, tana sayen su ne daga Amurka da sauran kasashen Turai, yayin da kaso 95 bisa dari na daukacin kayayyakin aikin soji na kasar Rasha da Ukraine ta lalata sun fito ne daga kasashen yammacin duniya, kana kaso 72 bisa dari na sassan makaman da Rasha ke kerawa sun fito ne daga kamfanonin Amurka.
A matsayinta na kasa mai hangen nesa da mutunta doka, kasar Sin ba ta taba samar da makamai ga kowane bangare na rikicin Ukraine ba, tana kuma tantance, da takaita kayan ayyuka da ake iya amfani da su a aikin soji da na farar hula.
A daya hannun kuma, Sin da Rasha na gudanar da hada-hadar cinikayya da tattalin arziki a bude, tare da biyayya ga dokoki da ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO. Yayin da a nasu bangare Amurka da ’yan koren ta, ke karya wadannan dokoki ta hanyar kakkabawa kamfanonin Sin takunkumi, da kuma nuna rashin sanin ya kamata wajen kitsa karairayi, da munafurci, da nufin shafawa kasar Sin bakin fenti, to amma dai bahaushe kan ce “Munafurci dodo ne mai shi ya kan ci”, kuma “Kowa zai gina ramin mugunta to ya gina shi gajere”, domin mai yiwuwa shi ne zai fada cikin sa!