Wasu fusatattun masu zanga-zanga sun isa gidan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ke Daura, a jihar Katsina ranar Alhamis.
Masu zanga-zangar, da yawansu, sun shiga zanga-zangar adawa da matsin rayuwa mai taken #EndBadGovernance da ake yi a fadin kasar.
- Ɓata-gari Sun Cinna Wa Sakatariyar APC Wuta Tare Da Lalata Kadarorin Gwamnati A Jigawa
- Zanga-zanga: Ɓata-gari Sun Lalata Tare Da Wawushe Kadarorin Gwamnati A Kaduna
Zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali a wasu jihohin, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane tare da tilastawa akalla gwamnoni uku kafa dokar hana fita ta awa 24.
‘Yan zanga-zangar da suka yi yunkurin kutsawa gidan tsohon shugaban kasar, sun ce, sun gaji da matsin rayuwa da tabarbarewar tattalin arzikin kasar ke ciki.
Wani ganau ya shaida wa Jaridar Daily Trust ta wayar tarho a ranar Alhamis cewa, “An kunna wuta a kofar gidan tsohon shugaban kasar sannan matasan suna ta rera waka da karfi.”
A cikin wani faifan bidiyo da Daily Trust ta samu, an ga matasa da dama suna ta rera waka da cewa:
“Bama yi! Bama yi! Bama yi!,”
Har sai da wani da ba a san ko wanene ba ya fito daga gidan Buhari ya kwantar da hankalin masu zanga-zangar da ya musu jawabi.
Bayan haka, fusatattun matasan sun nufi fadar Sarkin Daura, Alhaji Farouk Umar Farouk.
Rahotanni sun bayyana cewa, jami’an tsaro sun harbi daya daga cikin matasan a kafa yayin da suke kokarin tarwatsa su amma masu zanga-zangar suka ki ja da baya.
Talla