Gammayyar manyan kungiyoyin arewa da suka hada da Kungiyar Dattawa Arewa ta NEF da Kungiyar Tuntuba ta Arewa ta ACF sun nuna rashin amincewarsu da shirin Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na mayar da wasu sassan Babban Bankin Nijeriya (CBN) da kuma Hukumar Kula Filayen Jiragen Saman Nijeriya (FAAN) daga Abuja zuwa Legas.
Al’ummar yankin arewa da dama sun yi tir da wannan shirin, inda suke cewa, ana neman cimma wata manufa ce ta durkusar da tattalin arzikin arewa a kaikaice.
Da yake mayar da martani kan lamarin a cikin shirin Talabijin na intanet na LEADERSHIP, Barka da Hantsi Nijeriya da ake gabatarwa a duk ranakun aiki, da misalign karfe 9 na safe, mai magana da yawun kungiyar NEF, Kwamrade Abdul-Azeez Sulaiman, ya ce ba kawai sun yi watsi da wannan yunkurin ba ne, abu ne da za su yi tsayin daka a kai har sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi.
“A halin yanzu kawunan al’ummar arewa a hade yake a kan kare muradunta, za a iya fahimtar haka idan aka lura da cewa, a halin yanzu kungiyar sanatocin arewa sun shiga wannan maganar har sun nemi ganawa da Shugaban Kasa Tinubu don dakile shirin mayar da wadannan ma’aikatu Legas.
“Hujjar cunkoso da ake bayarwa na mayar da wadannna sassan ma’aikatu ba karbabbe ba ne, musamman ganin ai cukoson Legas ne ya haifar da samar da Abuja a matsayin sabon babbar birinin tarayya, Abuja kuma na da issassun filayen da za a yin kowanne irin gini don samar da mafita ga ikirarin cunkoso da suke yi.
“Wata makarkashiya ce daga yankin kudu maso yammacin kasar nan na mayar da al’ummarmu baya, musamman mata masu aiki a wadannan wuraren, mun samu labarin a halin yanzu da dama daga cikin su sun mika takadun neman barin aiki don ba za su iya barin iyalansu su koma Legas da sunan aiki ba,” in ji shi.”
Ya kuma bayyana cewa, babbar matsalar da yankin arewa ke fuskanta a halin yanzu ita ce rashin shubagani masu kishin yankin, domin shugabanin da ake da su a wanna zangon ba muradun arewa ke a gabansu ba, tara abin duniya ne kawai a gaban su, ba kamar shugabanni irin su marigayi Sir Ahmadu Bello Firimiyan farko na yankin arewa ba. “Abubuwan da shugabanin farko suka samar wa arewa don ci gaban al’umma duk an lalata su, kamar Bankin Arewa da sauran su” In ji shi
Ya kuma nemi al’ummar arewa su dunkule wuri daya ba tare da nuna bambanci kabila ko addini ba, ‘’ta haka za mu dawo da martabar al’ummarmu da kuma tabbatar da ci gaban yankinmu” in ji shi.
Daga karshe ya nemi al’ummar yankin arewa su bayar da dukkan gudummawar da ake bukata don yaki da mastalar tsaro da ke neman durkusar da yankin.
A nata bangaren kuwa, Kungiyar ACF ta bayyana cewa, shawarar CBN ta mayar da wasu sassa zuwa Legas ba an yi ba ce saboda ci gaban Nijeriya da kuma kishin kasa ko kuma domin warware wasu matsalolin da aka kasa warwarewa, sai dai don a cutar da al’ummar arewa da wasu sassan Nijeriya.
A takardar sanawar da kungiyar ACF ta fitar wanda ke dauke da sa hannun sakataren watsa labarunta na kasa, Farfesa T. A. Muhammad-Baba, ta ce, suna kallon wannan shiri a mastsyin wani kokari na ware arewa daga shiga harkokin tattalin arzikin kasa da kuma mayar da al’ummar arewa baya, ta kuma kara da cewa, ta samu wani bayanin sirri na wata wasika da wani kamfani mai suna ARFF ya rubuta wa ministan sufurin jiragen sama inda yake neman a dauke wani aiki da aka tsara yi a tashar jiragen sama na Katsina zuwa kudancin kasar nan ko kuma Abuja. Takardar ta kuma bayar da shawarar a mayar da aikin zuwa Legas, Ibadan ko Inugu.
“Yana da sauki a yi watsi da wannan shirye-shiryen na mayar da wasu ma’aikatu zuwa kudancin Nijeriya da CBN da FAAN suka fara, amma dole mu kalli shirin a matsayin shiryayyen lamari na ware yankin arewa, ko kuma ya zama wani sabon ajanda ne na mayar da al’ummarmu baya. A lokacin mulkinsa karo na farko a 1999, tsohon shugaban kasa Obasanjo ya umarci mayar da Hukumar Kula da Tashoshin Jiraghen Ruwan Nijeriya (NPA) da Hukumar Kula da Harkokin Kasashen Waje (NIIA) daga Abuja zuwa Legas.
“A yau kusan dukkan hukumomin da suka shafi teku suna garin Legas duk da cewa, a kwai wasu sassan kasa da za su iya daukar masaukin wadannan ma’aikatu.”
Sanarwa ta kuma ce, nasarar da aka samu ta gano man fetur a yankin kogin Kolmani na Jihar Gombe ya karyata masu ikiirarin cewa, babu man fetur a yankin arewa.
“Wadanna hujjojin sun sanya kungiyar ACF ba ta yarda da shirin mayar da wasu hukumomin gwamnati zuwa Legas ba”.
A kan haka ACF ta yi kira na musamman ga gwamnatin tarayya da majalisar kasa da kuma dukkan hukumomin da suke da hannu a wanna Shirin da su janye , su kuma dauki dukkan mataksn da suka kamata na kawo karshen cunkoson da suke fakewa da shi, baya ga haka ma akwai issassun filaye a Abuja da za a iya gina duk abin da ake bukata don ci gaban kasa.
“Kungiyar ACF na tunatar da al’umma cewa, fiye da shekara 20 da suka wuce aka dawo da mazaunin birinin tarayya Abuja ta hanyar doka kuma wannan dokar tana nan har zuwa yanzu, duk da cewa, wasu da dama ba su ji dadin haka ba,” in ji sanarwar.
Jim kadan dai bayan fitar da sanarwar hukumar gudanarwar CBN na mayar da wasu sassan Babban Bankin zuwa Legas ne sai kuma ga wata sanarwa daga ma’aikatar Sufurin Jiragen sama inda ta sanar da aniyyarta ta mayar da wasu sassan Hukumar Kula da Filayen Jiaragen Sama (FANN) zuwa Legas. A cewarta, an yanke shawarar haka ce saboda rashin isassun ofishoshi a Abuja da kuma yawan aikin da ake fuskanta a bangaren hukumar na Legas.
Bayanin ya kuna nuna cewa, daga cikin manyan daraktoci 40 da hukumar ta nada a kwanan nan, 8 ne kawai suka fito daga arewacin Nijeriya, wanda hakan ke nuna alamun kamar akwai lauje cikin nadi.