• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Murabus Ɗin Ganduje: ‘Yan Kwankwasiyya Na Shirin Ɗaukar Wani Mataki

by Sulaiman
4 months ago
Kwankwasiyya

Magoya bayan tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso na shirin daukar mataki na gaba biyo bayan murabus din da abokin hamayyarsa, Dr. Umar Abdullahi Ganduje ya yi a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Tun hawansa karagar mulki, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sha ganawa da Kwankwaso, inda suka tattauna batun sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa APC. Sai dai masana na ganin Kwankwaso ba zai iya shiga APC ba yayin da abokin hamayyarsa kuma tsohon mataimakinsa, Ganduje ne ke shugabantar jam’iyyar.

  • Gwamna Yusuf Ya Jagoranci Tawagar Kano Zuwa Jana’izar Marigayi Aminu Dantata A Madina
  • An Sauya Sunan Makarantar Wasanni Don Girmama Ƴan Kano Da Suka Yi Hatsari

A yanzu da Ganduje ya bar kujerar shugabancin jam’iyyar APC na kasa, magoya bayan Kwankwaso sun ce a shirye suke na bin wani mataki na gaba.

LABARAI MASU NASABA

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

Magoya bayan Kwankwaso, wadanda aka fi sani da Kwankwasiyya, sun yi ikirarin cewa Ganduje ya bai wa mutanen Kano kunya, shi ya sa ya yi murabus.

Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Hashimu Dungurawa, wanda ya yi magana a madadin magoya bayan Kwankwaso, ya bayyana murabus din Ganduje a matsayin kwaso abin kunya ga Kano.

Ya bayyana cewa, an sami Ganduje ne da son yin almundahana, musamman a lokacin zaben shugabannin jam’iyyar da aka kammala kwanan nan.

Dungurawa ya yi wannan ikirarin ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake amsa tambayoyi daga LEADERSHIP game da matakin da jam’iyyar za ta dauka na gaba bayan faruwar wannan lamari.

Ya ce, kafafen yada labarai sun rika yada cewa, Ganduje ya yi murabus ne saboda zargin karkatar da kudi, inda ya ce murabus din nasa ba na kashin kansa ba ne.

Sai dai ba zai iya cewa ko wannan lamarin zai iya sa jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso sauya sheka zuwa APC ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi
Labarai

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

October 19, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza
Labarai

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

October 19, 2025
Nijar
Labarai

Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani

October 19, 2025
Next Post
Cikar MDD Shekara 80: Nasarorinmu Sun Kara Mana Kaimi Da Kyakkyawar Makoma A Nan Gaba

Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

October 19, 2025
Yadda Ake Alkaki

Yadda Ake Alkaki

October 19, 2025
Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (2)

October 19, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

October 19, 2025
Nijar

Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani

October 19, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

October 19, 2025
gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.