A wannan makon ne hasashen da LEADERSHIP Hausa ta yi a makon da ya gabata cewa kujerar Sanata Abdullahi Adamu ta shugabancin APC tana-kasa-tana-dabo ya tabbata inda ya yi murabus tare da sakataren jam’iyyar Omisore.
Ganin cewa ba wannan ne karon farko ba, tun bayan da Nijeriya ta dawo mulkin dimokuradiyya, shugabannin jam’iyyu ba su cika karko a kan kujerunsu ba, tun daga jam’iyya mai mulki har zuwa sauran jam’iyyun adawa. Tambayar da galibin ‘Yan Nijeriya ke yi ita ce, a ina gizo yake sakar, daga yanayin mukamin ne ko kuma daga shugabanin ne. Mun leka jam’iyyun domin waiwayen abubuwan da suka faru.
Jam’iyyar PDP
Tun da aka kafa jam’iyyar PDP a 1998, Sanata Ahmadu Ali ne kadai ya kammala wa’adin farko na shugabancin jam’iyyar. Sauran dai duk tsige su aka yi ko kuma matsin lamba da tilasta musu yin murabus nan take.
Ana ganin daga cikin abubuwan da ke hana shugabannin karko a mukaminsu har da katsalandan daga fadar shugaban kasa da kuma karfin ikon jam’iyyar a jihohi tsakanin gwamnoni da shugaban jam’iyyar na kasa.
Jam’iyyar PDP ta yi shugabanni daban-daban wadanda suka hada da Cif Solomon Lar, Barnabas Gemade, Cif Bincent Ogbulafor, Cif Okwesilieze Nwodo, Alhaji Bamanga Tukur, Cif Audu Ogbe, Uche Secondus da kuma Dakta Iyorchia Ayu dukkansu sun bar shugabanci saboda wani dalili ko kuma wasu dalilai masu yawa.
Solomon Lar
An zabi Cif Lar a matsayin shugaban jam’iyyar PDP a tsakanin 1998 zuwa 2002.
Bayan shafe watanni a kan mukamin shugabancin jam’iyyar, ya samu sabani da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo kan ikon shugabancin jam’iyyar.
Duk da kasancewar Lar a matsayin daya daga cikin wadanda suka yanke wa PDP cibiya, amma haka bai hana shi taba kasa ba sakamakon rigimar nuna karfin iko da jam’iyya da ta barke tsakaninsa da Obasanjo musamman ma ta bangaren majalisar kasa. An maye gurbin Lar da Barnabas Gemade, dan siyasa daga Jihar Benuwai.
Barnabas Gemade
Kwadayin neman wa’adi na biyu a 2023 ya karfafa dangantaka tsakanin Obasanjo da Gemade, sai dai daga bisani da Obasanjo ya fahimci kamar Gemaden ba zai biya masa bukata ba bisa zargin ya kasa hada kan jam’iyyar, sai ya bukaci ya sauka daga kan mukaminsa.
Domin dadada wa mutanen Jihar Benuwai, Obasanjo ya maye gurbin Gemade da Audu Ogbeh, wanda ya kasance cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, inda shugaban ya yi amannar zai iya taimaka wa jam’iyyar ta samu nasara a zaben 2003.
Wa’adin shugabancin Ogbeh ya zama mai ban mamaki saboda kokarinsa na tabbatar da samun cin gashin kai sabanin wanda ya gabace shi, ya jefa shi cikin matsala. An yi zargin cewa an tilasta masa yin murabus ne bayan da ya shawarci tsohon shugaban kasa Obasanjo ya dauki mataki kan rikicin da ya dabaibaiye jam’iyyar a Jihar Anambra, inda aka ce aminin shugaban kasa, Chris Uba ya caccaki Gwamna Chris Ngige tare da tilasta masa yin murabus.
A karshe dai an kori Ogbeh a watan Disambar 2004, inda Obasanjo ya maye gurbinsa da Ahmadu Ali, wanda ya dade suna aikin soja tare.
Ahmadu Ali
Har zuwa yau, babu wani shugaban jam’iyyar PDP da aka zaba ya kammala wa’adin mulkinsa sai Ahmadu Ali. Bayan cikar wa’adinsa ne aka nada shi shugaban hukumar kayyade farashin man fetur (PPPRA).
Prince Bincent Ogbulafor
Prince Bincent Ogbulafor, ya amsa shugabancin jam’iyyar PDP daga hannun Ali, inda shi ma aka tilasta masa yin murabus sakamakon takaddamar da ta barke tsakaninsa da gwamnan jiharsa ta Abiya, Theodore Orji.
Bamanga Tukur
Bamanga Tukur ya fara samun matsala ne tun daga jiharsa ta Adamawa, inda tsohon Gwamna Murtana Nyako ya kalubalanci shugabancinsa a jam’iyyar ta PDP.
Gabanin zaben 2015, mafi yawancin gwamnonin PDP ciki har da Nyako sun bukaci a tsige Tukar daga mukaminsa, kasancewarsa babban aminin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da zai iya ba shi damar neman wa’adi na biyu. Amma kuma da Jonathan din ya fito fili ya nuna muradinsa na takara duk da ana ganin dan arewa ya kamata a bai wa takara a 2015, Bamangan da kansa ya ajiye shugabancin jam’iyyar domin rigakafin a rika masa Kallon maci-amanar-arewa.
Uche Secondus
Dangane da lamarin Secondus kuwa, wasu jiga-jigai daga yankin kudu karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike suka yi uwa suka yi makarbiya wajen ganin ya hau kujerar shugabancin jam’iyyar domin kare muradunsu na siyasa. Amma a lokacin da suke ganin reshe ya juye da mujiya, sai suka jagoranci tuntsurar da shi, duk kuwa da cewa yana dab da kammala wa’adinsa. Daga mazabarsa ta lamba 5 da ke garin Ikuru a karamar hukumar Andoni ta Jihar Ribas suka tandara shi da kasa.
Dakta Iyorchia Ayu
Bayan tsige Secondus ne aka nada Dakta Iyorchia Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar PDP. Shi kuma tashi rigimar ta fara ce yayin da aka zarge shi da kin mutunta yarjejeniyar raba mukaman siyasa da yin karfa-karfa a zabukan da suka gabata na 2023 da kuma takun-saka tsakaninsa da gwamnan jiharsa, Samuel Ortom, wadannan na daga cikin abubuwan da suka haifar masa da matsala.
Daga karshe dai Ayu ya bi sahun sauran shugabannin jam’iyyar da suka gabace shi, inda yana ji yana gani ya bar kujerar shugabancin da karfi da yaji.
Jam’iyyar APC
A bangaren jam’iyyar APC kuwa, cikin shekaru 10, jam’iyyar ta yi shugabanni har guda shida.
An dai kafa jam’iyyar APC ce a 2013, domin ta kwace mulki daga hannun jam’iyyar PDP mai mulki. Hakan dai ya zo ne sakamakon hadewar wasu jam’iyyun siyasa wuri daya, wadanda suka yi maja domin yi wa PDP taron dangi.
Jam’iyyun da suka dunkule wuri daya sun hada da ACN, CPC, ANPP, da wani bangare na APGA da kuma sabuwar PDP (New PDP).
Bisi Akande
An cimma matsayar nada Akande ne a matsayin shugaban riko na jam’iyyar APC na kasa a yayin wani taron sirri da masu ruwa da tsaki suka yi a Abuja, wanda ya samu halartar jiga-jigan ‘yan siyasa daga cikin jam’iyyar.
Umarnin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayar na jam’iyyun majar su kafa majalisar zartaswa ta kasa a wani bangare na tsarin rajista ne ya kawo karshen shugabancin Bisi Akande.
John Odigie-Oyegun
Oyegun, tsohon gwamnan Jihar Edo shi ne zababben shugaban jam’iyyar APC na kasa na farko bayan yi mata rajista.
Ya gaji Bisi Akande ne ta hanyar sahalewar wakilai masu zabe a babban taron jam’iyyar na farko da ya gudana a dandalin Eagles Skuare da ke Abuja a watan Yunin 2014.
Jagoran jam’iyyar na kasa kuma Shugaba Bola Tinubu shi ne ya tallafa wa Oyegun ya hau kujerar shugabancin.
Ya kammala wa’adinsa na farko har aka sanar da kara masa shekara daya, amma hakan bai yiwu ba saboda rikice-rikicen cikin gida da jam’iyyar ta fuskanta, daga bisani tilas ya ajiye shugabancin a watan Yunin 20218.
Adams Oshiomhole
Oshiomhole, kamar Oyegun, shi ma tsohon gwamnan Jihar Edo ne wanda ya gaji kuejarar shugabancin APC a watan Yunin 2018. Tsohon shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa, ya samu goyon bayan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da wasu jiga-jigan jam’iyyar.
Sai dai kuma daga baya rikici ya barke a jam’iyyar, wanda ya kai ga korar shi da sauran mambobin kwamitin zartarwa na jam’iyyar.
Kwamitin zartarwa na jam’iyyar wanda shi ne matsayi na biyu wurin yanke hukunci a jam’iyyar, ya tsige shugabancin Oshiomhole a ranar 25 ga Yunin 2020, sakamakon zargin yin amfani da ofishinsa ba bisa ka’ida ba da kuma kasa hada kan ‘ya’yan jam’iyyar.
Oshiomhole tare da tawagarsa sun kwashe tsawon shekara biyu ne kacal daga cikin wa’adin shugabancinsu na shekaru hudu sakamakon barkewar rikici a cikin jam’iyyar.
Mai Mala Buni
Bayan rushe shugabancin Adams Oshiomhole, an bai wa gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni rikon kwarya na shugabancin jam’iyyar.
A farko dai an bai wa kwamitin da Buni yake jagoranta wa’adin watanni shida tun daga ranar 25 ga watan Yunin 2020, kafin a tsara yadda za a gudanar da babban taron jam’iyyar da zai bayar da damar zaben shugaba. Amma a watan Disambar 2020, an kara tsawaita shugabancin kwamitin na tsawon wata shida domin samun damar sasanta fusatattun ‘ya’yan jam’iyyar kafin gudanar da babban taro.
Bayan shudewar wata shida, kwamitin bai kammala aikinsa ba na shirya babban taron jam’iyyar sakamakon rajistar mambobin jam’iyyar da aka kammala a ranar 31 ga Maris, 2021.
Shugaba Buhari ya kara wa’adin shugabancin kwamitin a watan Disamba har sai illa ma sha Allahu. Kwamitin da Buni ya jagoranta ya gudanar da aikin sulhunta ‘ya’yan jam’iyyar a dukkan fadin kasar nan, wanda ya kafa kwamiti karkashin jagorancin tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu.
A wancan lokaci, APC ta samu nasarar janyo jiga-jigan ‘yan jam’iyyar PDP da suka hada da Gwamna Ben Ayade na Jihar Kuros Ribas da Dabid Umahi na Jihar Ebonyi da Bello Matawalle na Jihar Zamfara da tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara da tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Cif Barnabas Gemade da sanatoci da sauran jiga-jigan ‘yan siyasa zuwa cikinta.
Daga karshe kwamitin Buni shi ma ya yi tangal-tangal, kasancewar bayan ya tafi neman magani a kasar waje, sai aka ji tsohon gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya hau kujerarsa, sai dai ba ta baci ba, daga baya sun gyaro ta har Bunin ya samu nasarar gudanar da babban taron jam’iyyar wanda aka zabi Abdullahi Adamu a matsayin shugaba.
Abdullahi Adamu
Adamu ya zama shugaban jam’iyyar APC ne a babban taron jam’iyyar da kwamitin Buni ya shirya a dandanlin Eagle Skuare da ke Abuja a watan Maris, 2022.
Shugaban Buhari ya taimaka masa har ya samu nasarar zama shugaban jam’iyyar APC bayan an bukaci sauran ‘yan takara su janye masa.
Sai dai tuni wa’adin Adamu na shekaru hudu suka ruguje sakamakon murabus da ya yi a farkon makon nan bisa matsin lamba saboda wasu zarge-zarge da ake masa da suka hada da rashin goyon bayan wanda ya lashe zaben shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu lokacin da yake neman a tsayar da shi takara.
Haka nan a kwanan nan, mataimakain shugaban jam’iyyar na arewa maso yamma, Salihu Mohammed Lukman ya bukaci Adamu ya sauka daga mukaminsa domin maye gurbinsa da wani kirista.
Lukman ya kara da cewa sam babu adalci da daidaito kasancewar zababben Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu dukkansu Musulmai ne.
Duk da yake Adamu bai mayar da martani kan lamarin ba daga karshe dai ya yada kwallon mangwaro don yah uta da kuda tare da sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Iyiola Omisore.
Kwamtin zartarwa na jam’iyyar dai ya bai wa Sanata Abubakar Kyari rikon shugabancin jam’iyyar tare da dage taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar da aka so gudanarwa a ranakun 18 da 19 ga watan nan.
Jam’iyyar LP
Ita ma jam’iyyar LP wacce ba da dade da yin karfi ba tana cikin rikicin shugabanci a halin yanzu, wanda ake ganin cewa lamarin na ci gaba da ta’azzara tun bayan kammala zaben shugaban kasa.
Ko me ya sa shugabannin jam’iyyun ba su cika karko ba?
Malami a Jami’ar Abuja, Dakta Abubakar Umar Kyari, ya amsa da cewa rashin ingantaccen gudanar da dimokuradiyya ta cikin gida daga jam’iyyun ne ke haddasa rikici har ya yi awon gaba da kujerar shugaban jam’iyyar.
Kyari ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai ta wayar tarho, inda ya kara da cewa wasu jiga-jigai masu karfi ne suke yin katsalandan a cikin jam’iyyu tare da tantance abin da ya kamata a yi a cikin jam’iyya, sannan suna iya bakin kokarinsu wajen tusa bukatocinsu.
Ya ce, “Wannan shaida ce ta rashin dimokuradiyyar cikin gida a tsakanin jam’iyyun siyasa. Manyan ‘yan siyasa da ake kira ubangida a fadar shugaban kasa da gwamnoni ke juya manyan jam’iyyu irinsu APC da PDP.
“Shugaban kasa da tawagarsa ne ke tantance abubuwan da za a yi a jam’iyya a matakin kasa. Domin haka idan wadannan ubangida suka raba gari da shugabannin jam’iyya, sai su cire su daga kan mukamansu.” Ya bayyana.