Akalla mutum 11 ne suka rasu a ranar Alhamis yayin da wasu 8 suka samu raunuka a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a Jihar Edo.
Hatsarin ya faru ne a kan titin Benin zuwa Legas wanda ya hada da wata motar bas kirar Toyota Hiace mai daukar mutum 18 da wata motar Dangote.
- Yadda Tallafin Gaggawa Da Kasar Sin Ta Samarwa Zimbabwe Ya Kara Fito Da Manufar Kawancen Gargajiya Tsakanin Sassan Biyu
- Malaman Addinin Kirista A Kaduna Sun Yi Allah Wadai Da Kone Alkur’ani A Sweden
LEADERSHIP ta tattaro cewa, hatsarin ya auku ne da misalin karfe 11 na safe a kan gadar kogin Ovia wanda ya yi kaurin suna wajen hadarurruka sakamakon lalacewar wani bangaren titin da ke kusa da gadar kogin.
Wani ganau wanda ya shaida afkuwar hadarin ya ce “Mota Bas (Toyota Hiace) da ta fito daga gabashin jihar Edo yayin da ta dan jinkirta gudunta sabida lalacewar hanyar da ke kusa da gadar kogin Ovia amma motar Dangote da ke kan gudu ta yi awon gaba da bas din bayan ta buge wata mota kirar KIA.”
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Edo, Paul Okpe, wanda ya tabbatar da faruwar hadarin, ya ce “mun samu labarin hadari a kan gadar kogin Ovia a safiyar yau (Laraba), wata babbar mota ce ta ci karo da wata mota kirar Toyota Hiax, Mutane 11 sun rasu tare da raunata mutane takwas.
“Duka wadanda lamarin ya rutsa da su an kaisu Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin (UBTH)”.