Akalla mutane 132 ne suka mutu a wata girgizar kasa da ta afku a wani yankin Nepal a jiya Asabar, yayin da jami’an tsaro suka yi gaggawar kai daukin ceto.
Hotunan bidiyo da hotuna da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna yadda mutanen yankin ke tona baraguzan gine-gine a cikin duhu don ceto wadanda ke da sauran numfashi acikin baraguzan gidaje da gine-gine da suka ruguje.
Gidaje da dama sun lalace yayin da jami’an kai daukin gaggawa ke ta kokarin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp