Aƙalla mutane 14 ne suka mutu a wani mummunan haɗarin mota da ya rutsa da wata motar dakon shanu 35 da fasinjoji a kan titin Kontagora da ke Jihar Neja.
Haɗarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safe ranar Talata, 17 ga Nuwamba, 2026, a kusa da garin Ibeto, lokacin da motar ƙirar DAF ke kan hanyarta daga ƙaramar hukumar Koko ta Jihar Kebbi zuwa Legas.
Majiyoyin ƴansanda sun bayyana cewa wata motar da ba a gano ko ta wacece ba, wadda ke tafiya a hanya ɗaya da motar, ta yi ƙoƙarin wuce ta, amma ta goge gefenta. Hakan ya sa direban motar dakon shanun ya rasa iko da ita, kafin ta kife. Direban mai suna Umar, mai shekaru 45, da wasu fasinjoji 13 sun mutu a wurin da haɗarin ya faru.

Daga cikin waɗanda aka gano sun mutu akwai Anas Suleiman mai shekaru 25 da Sufiyanu Suleiman mai shekaru 40, dukkansu daga Koko, da kuma Salim Abu Dogo, Abubakar Shehu, Yahaya Abubakar da Manu daga Dankigari.
Sauran sun haɗa da Rufai Umar daga Bagudo, Faruk Tudu Kaoje, Umar Abubakar, Salisu Idry da Abubakar Alhaji. An sallami gawarwakin waɗanda iyalansu suka gane domin yi musu jana’iza bisa tsarin addinin Musulunci, yayin da aka ajiye gawarwaki biyu da ba a gano ko na su wanene ba a ɗakin ajiyar gawa na Babban Asibitin Kontagora.
Rahoton ya ce an gano motar da ake zargin ta yi ƙoƙarin wuce motar dakon shanun a Kaboji, cikin ƙaramar hukumar Magama, inda aka kai ta ofishin rundunar ƴansanda na yankin. Sai dai direban motar ya tsere kuma har yanzu ba a kama shi ba.
Rundunar ƴansandan Jihar Neja ta ce tana gudanar da bincike domin gano cikakken abin da ya haddasa haɗarin da kuma cafke direban da ya gudu.













