Mutane 16 ne suka mutu yayin da wasu biyar suka jikkata a wani hatsarin mota da ya afku a unguwar Epe da ke jihar Legas.
Hadarin mota da ya rutsa da motoci biyu da sanyin safiyar Talata a kan hanyar garin Alaro, Epe, ya shafi maza 23.
- Peter Obi Ba Ya Goyon Bayan IPOB – Baba-Ahmed
- Jirgin C919 Na Kasar Sin Ya Kammala Gwajin Ingancin Tashi
An bayyana cewa yayin da 16 suka mutu, biyar sun samu munanan raunuka, biyu kuma ba su samu rauni ba.
Da take tabbatar da afkuwar hatsarin, Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa reshen jihar Legas, ta ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 03:00 na dare, kuma ya faru ne sakamakon rashin ganin ido hanya sosai da tukin ganganci.
Kakakin FRSC, Olabisi Sonusi, ya fitar da sanarwa, inda ya ce an kwantar da mutane biyar da suka jikkata.
“Motocin da hatsarin ya rutsa da su, wata farar bas ce mai lamba KTN 262YJ da wata babbar mota kirar Articulated (Lambar rajista ba a san ko waye ba),” in ji sanarwar.
“Jami’an FRSC da sauran hukumomin bayar da agajin gaggawa suna nan a kasa, suna tabbatar da samun sauki cikin gaggawa tare da kwashe dukkan motocin da suka yi hatsarin.
“Saboda haka babban kwamandan hukumar kiyaye hadura ta kasa reshen jihar Legas, Cif Olusegun Ogungbemide, ya shawarci masu ababen hawa da su guji yin tafiyar dare a ko da yaushe saboda rashin iya gani hanya sosai.
“Ya kuma gargadi jama’a masu tuka ababen hawa a ko da yaushe da su kiyaye kayyade saurin gudu a irin wadannan yankuna.
“Ogungbemide kuma yana amfani da wannan kafar don jajanta wa iyalan mamatan tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki.”