Aƙalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu yayin da wasu huɗu suka jikkata a fashewar bam da ta auku a Konduga, jihar Borno, a ranar Litinin.
Wasu shaidar ganau sun bayyana cewa, wasu samari ne suka kawo bama-baman guda shida cikin gari suna ɗaukar su a matsayin tsofaffin ƙarafuna, ba tare da sun sani ba cewa abubuwan fashewa ne.
Fashewar ta faru ne a hanyar su ta zuwa Ajari, wani ƙauye da ke yankin Konduga, inda nan take mutane biyu suka mutu, yayin da aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Gwamnati na Konduga domin samun kulawa.
- Fim Babbar Hanya Ce Ta Nishaɗantar Da Al’umma -D Malam Dan Bola (2)
- Fim Babbar Hanya Ce Ta Nishaɗantar Da Al’umma -D Malam Dan Bola (2)
A wani labarin makamancin haka, rundunar Ƴansandan jihar Borno ta gano wani bama da bai kai ga fashewa ba (UXO) a gonar wani manomi a ƙaramar hukumar Dikwa.
Mai magana da yawun rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce an gano bama-baman ne bayan wani manomi, Babagana Kachalla, ya ba da rahoton wani abu da yake shakka a gonarsa.
Daso ya bayyana cewa tawagar ƙwararrun kwance ban (EOD) ta gudanar da aikin kwance bama-baman a wurin ba tare da wata matsala ba, sannan ta wayar wa al’ummar yankin kai kan illar bama-bamai da kuma hanyoyin da za su bi wajen kai rahoto idan sun gano irin waɗannan abubuwa masu haɗari.
Rundunar ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da yin iya ƙoƙarinta wajen kare rayukan jama’a a jihar.












