Hare-haren kunar bakin wake guda hudu a garin Gwoza na Jihar Borno, sun yi sanadin mutuwar mutane 20 tare da jikkata wasu 52, kamar yadda hedikwatar tsaro (DHQ) ta tabbatar. Â
Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne, ya bayyana cewa wadanda suka jikkata na samun kulawa a asibiti, yayin da kuma ya yi mika ta’aziyyasa ga iyalan wadanda suka rasu.
- Nijeriya Ta Kulla Yarjejeniyar Yakar Yunwa Da Saudiyya
- ‘Yan Ta’adda Sun Kashe ‘Yansanda 4 A Katsina
Ya yi nuni da cewa, hare-haren wani martani ne da ‘yan ta’adda suka kai sakamakon nasarar da dakarun soji ke samu a kansu a baya-bayan nan.
An fara kai hare-haren ne da misalin karfe 3 na rana, inda wata ‘yar kunar bakin wake ta yi basaja, ta tayar da bam a wajen wani biki a titin Mararaba Hausari.
Bam na biyu da ya tashi, ya faru ne bayan sa’o’i biyu, inda shi ma wani mutum ya yi basaja a matsayin mai yin ta’aziyya ya tayar da bam.
Bayan haka, yayin da aka sanar da dokar hana fita domin dakile asarar rayuka, bam na uku ya tashi tare da kashe soja daya da wasu dakarun hadin gwiwa biyu.
A cewarsa sun yi nasarar dakile hari na hudu, wanda ba a samu asarar rayuka ba.
Janar Buba ya bayyana kokarin da sojoji ke yi na daidaita al’amura da tsaro a yankin da harin ya faru.
Ya tabbatar da cewa rundunar soji na ci gaba da jajircewa wajen ganin ta kawar da barazanar ta’addanci.