Rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya, Abuja, ta tabbatar da rushewar wani gini mai hawa hudu ne a yankin Garki.
Sanarwar da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar ta ce ginin ya rushe ne ranar Litinin da daddare.
- Mutane 20 Sun Mutu, 52 Sun Ji Rauni A Harin Bam A Borno – DHQ
- Kwastam Ta Kama Bindigu A Tashar Jiragen Ruwa A Ribas
Ta ce bayan samun kiran waya kan lamarin, kwamishinan ‘yansandan Abuja, Benneth Igweh, ya tura jami’ansa zuwa wurin.
A cewar sanarwar, an kubutar da mutum uku daga cikin ginin da ya rushe, inda kuma aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa da lafiyarsu.
Sanarwar ta bayyana cewa rundunar ta ankarar da hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa domin su ɗauki ragamar zaƙulo mutanen da ƙasa ta birne.
Rundunar ‘yansandan ta kara da cewa an sanar da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da Hukumar Kula da Ci gaban Kasa ta Babban Birnin Tarayya Abuja, kuma jami’ansu sun wajen domin gudanar da nasu aikin.