Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ta tabbatar da mutuwar mutane 25 bayan da wani jirgin ruwa ya nutse a yankin Gbajibo da ke Karamar Hukumar Mokwa.
A ranar 1 ga watan Oktoba, wani jirgin ruwa mai dauke sama da fasinjoji 200 da ya taso daga Gbajibo da nufin zuwa wajen Maulidi ya kife.
- Kungiyar Ma’aikatan Jinya Da Ungozoma Na Shirin Tsunduma Yajin Aiki A Kano
- ‘Yan Ta’adda 20 Sun Kashe Juna A Wata Arangama Da Ta Kaure Tsakanin Su A Katsina
Darakta Janar na NSEMA, Abdullahi Baba-Arah, ya ce hukumar ta fara gano gawar mutane tara ne, sannan ta sake gano wasu gawarwakin wasu mutane 16 a yayin aikin ceto da ta gudanar.
Cikin wadanda suka rasu akwai maza 21 da mata hudu.
Har yanzu ana ci gaba da neman sauran fasinjoji 125 da suka bace.
“Gawarwaki 16 aka gano zuwa yanzu, wadanda suka hada da mata biyu da maza 14,” in ji sanarwar.
NSEMA ce ke jagorantar aikin ceto tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Sufuri ta Jihar, da sauran al’umma masu son taimakawa.
Ya kara da cewa, aikin ceto na ci gaba da gudana, yayin da jihar ke jimamin mutuwar wadanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan hatsari.