Akalla mutane uku ne suka jikkata yayin da manoma da makiyaya suka yi arangama a dajin Baranda da ke karamar hukumar Kiyawa a Jihar Jigawa.
Kakakin rundunar DSP Lawal Shiisu ne, ya tabbatar da hakan a jihar a ranar Alhamis.
- Gwamnatin Kano Za Ta Dauki Masu Gadi 17,600 Don Bai Wa Makarantun Jihar TsaroÂ
- Ana Ganawa Tsakanin ASUU Da Gwamnatin Tarayya
“Mun samu labarin faruwar lamarin a ranar Talata, da misalin karfe 2:15 na rana,” in ji kakakin.
“Da samun rahoton, jami’in ‘yansanda na sashen Kiyawa, tare da tawagar ‘yan sintiri, suka garzaya wajen. Tawagar ta hada da jami’an karamar hukumar Kiyawa, shugabannin Kautal Hore da Miyetti Allah, kungiyar manoman Nijeriya (AFAN), da shugabannin kauyen da abin ya shafa.
“A yayin tattaunawa a tsakanin masu ruwa da tsaki, rundunar ta gano mutane uku da suka jikkata tare da ceto wasu shida da ake shirin kai wa hari,” in ji shi.
Kakakin ya kara da cewa an garzaya da wadanda abin ya shafa zuwa asibiti inda aka yi musu magani.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa wasu makiyaya biyu na da hannu a harin, amma rundunar za ta gayyace su domin amsa tambayoyi.