Akalla mutane 32 da suka kunshi yara 20 da iyaye 12 ne suka rasu a wani hatsarin kwale-kwale a garin Ibbi da ke karamar hukumar Ibbi a Jihar Taraba.
An samu cewa, kwale-kwalen yana jigilar masunta ne fiye da 50 daga garin Ibbi zuwa Gabashin Nijeriya a ranar Asabar din da ta gabata don yin kamun kifi a lokacin da ya kife a kusa da Zabu da ke tsakanin iyakar Taraba da Benuwai, a gabar kogin Benue.
- Zaben Kogi: INEC Ta Musanta Zargin Sauya Kuri’un Da Ta Dora A Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe
- Zaben Kogi: INEC Ta Musanta Zargin Sauya Kuri’un Da Ta Dora A Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe
Wani mazaunin garin Ibbi, Malam Ibrahim Ibbi, ya ce yara 20 da iyaye 12 ne suka mutu a hatsarin.
Gwamnan jihar, Agbu Kefas, ya bayyana lamarin na baya-bayan nan a matsayin wani abin takaici, kwanaki kadan bayan faruwar makamancin hakan a Karim Lamido.
Ya jajantawa al’ummar Ibi da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.