Tankar mai ta fashe da misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar Asabar a mahaɗar Dikko da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a Ƙaramar Hukumar Gurara ta Jihar Neja, inda mutane 60 suka rasu, wasu da dama kuma suka jikkata.
Yawancin mutanen da suka rasa rayukansu sun mutu ne sakamakon mutanen da suka je deɓo mai daga tankar kafin ta fashe.
- Tattalin Arzikin Sin Ya Kasance Cikin Tagomashi A Shekarar 2024
- Ƴansanda A Gombe Sun Yi Holar Masu Laifuka
Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), Kumar Tsukwam, ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma adadin waɗanda abin ya shafa.
Ya bayyana cewa ana ci gaba da aikin ceto, kuma an ɗauki matakan tabbatar da tsaron masu amfani da hanyar.
Sannan, an kawar da cunkoson ababen hawa a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Ya ce suna ci gaba da bincike kan yadda mai ya fara zuba daga motar, da kuma yadda mutane suka yi tururuwar ɗiba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp