Akalla fasinjoji bakwai ne aka tabbatar da mutuwarsu a ranar Lahadin da ta gabata, yayin da wasu biyar suka samu kone-kone daban-daban a lokacin da wata motar bas ta kasuwanci ta tashi da wuta a gefen Iyana Oworo na jihar Legas.
Fasinjojin bakwai sun mutu bayan da motar bas din ta kama wuta, inda suka kashe mata hudu, maza biyu da kuma yaro namiji.
- Bene Ya Rufta Da Mutum Tara A Jihar Legas
- Kasuwannin Jihar Legas Sun Bunkasa A Karkashin Jagorancinmu –Shehu Samfam
Wadanda suka shaida lamarin sun ce direban motar bas din mai lamba KJA 699 GY ya tsere da wasu kone-kone, sannan jami’an hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASAMBUS) suka ba wani fasinja kulawa a wurin.
An bayyana cewa, an garzaya da wasu manya mata uku da jami’an agajin gaggawa suka ceto zuwa babban asibitin Gbagada yayain hadarin.
An ce motar bas din tana kan hanyar zuwa Iyana Oworonshoki ne, kwatsam ta samu matsalar wutar lantarki, nan take ta kama wuta.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA), Dakta Olufemi Oke-Osanyintolu, ya ce mutane bakwai ne suka mutu a hadarin.
A cewar Oke-Osanyintolu, an mika gawarwakin mamatan ga sashin kula da lafiyar muhalli na jihar (SEHMU) domin samun kulawar da ta dace a lokacin da iyalansu za su iya tantance su.
Ya ce, “Da isa wurin, an gano wata motar bas mai dauke da fasinjoji 14 Mazda mai lamba KJA 699 GY ta kone.
“Bincike da aka yi a wurin ya nuna cewa lamarin ya faru ne saboda rikon sakainar kashi da kuma wuce gona da iri da direban ya yi wanda ya yi sanadiyar tashin gobarar da fasinjoji 12 ta ritsa da su.
“An yi shiri da jami’an hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Jihar Legas (LASTMA) a wurin da lamarin ya faru domin kwato motar da ta kone daga kan hanya.
“LRT tare da LRU Paramedics LASTMA, LASAMBUS, SEHMU, da kuma ‘yan sandan Nijeriya suka kai dauki a wurin. An bude wani bangare na hanyar don wucewar ababen hawa.”