Hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta kasa (NCDC) ta tabbatar da bullar cutar zazzabin Dengue a Jihar Sakkwato.
Babban Daraktan hukumar, Dakta Ifedayo Adetifa wanda ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja, ya ce mutum 71 ake zargin sun kamu da cutar.
- Guardiola Ya Soki ‘Yan Wasan Manchester City Kan Rashin Kwazo
- Kayan Masarufi Sun Sake Tashin Gwauron Zabi A NijeriyaÂ
An tabbatar da mutum 13 sun kamu sai dai babu rahoton asarar rai daga kananan hukumomin jihar uku da aka samu bullar cutar.
Adetifa ya bayyana cewa galibin mutanen da ake zargin sun kamu da cutar ‘yan shekara tsakanin 21 da kuma 40 ne, inda ya ce an gano hakan cikin watan Nuwamban 2023.
Ya ce barkewar cutar a yanzu yana mataki na matsakaici la’akari da binciken da aka yi game da hatsrin cutar.
Ya kuma ce akwai isassun kayan aiki da kuma ma’aikatan lafiyar da za su dukufa ko da an samu barkewar cutar a sauran jihohin kasar.
Zazzabin Dengue cuta ce da sauro ke yada ta a yankuna masu zafi da wuraren da ke makwabtaka da su.
Alamominta sun hada da zazzabi da ciwon kai da tashin zuciya da amai da ciwon gabobi da fitowar kuraje, a wasu lokuta kuma, tana iya janyo mutuwa.
Adetifa ya shawarci ‘yan Nijeriya musamman mazauna Jihar Sakkwato da su bi dukkan matakan kariya kamar sanya kayan da za su rufe jikinsu domin kare kansu daga cizon sauro sannan su kwanta a gidan sauro mai magani.
A watan Oktoba ne, hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta yi gargadi cutar na iya bulla a kudancin Amurka da kudancin Turai da wasu sassan Afirka.