Akalla mutane tara ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu uku suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a kan hanyar Kano zuwa Zariya.
Kakakin hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC), reshen Jihar Kano, Abdullahi Labaran ne, ya sanar da hakan cikin wata sanarwa a ranar Laraba.
- Wani Asibiti A Kano Ya Ƙaddamar Da Na’urar Kula Da Jarirai Irinta Ta Farko A Arewacin Nijeriya
- Xi Jinping Ya Taya Murnar Budewar Dandalin Mata Na SCO
Ya bayyana cewa hatsarin ya auku ne a ranar Laraba 10 ga watan Satumba, 2024 a karamar hukumar Kura da ke Jihar Kano.
Labaran, ya bayyana cewa hatsarin ya rutsa da wata babbar mota da babura uku, wanda aka samu jimilla mutane 12 a hatsarin.
“Abin takaici mutane tara ne suka rasa rayukansu a hatsarin, yayin da wasu uku suka samu raunuka, amma an kai su babban asibitin Kura domin samun kulawar likitoci.
“Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa hatsarin ya faru ne bisa kuskurem
“Kwamandan hukumar, reshen Jihar Kano, Kwamanda Ahmed Mohammed, ya jajanta wa iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata.
“Ya kuma nanata muhimmancin bin ka’idojin tuki, sannan ya bukaci direbobi su kiyayi gudun wuce kima yayin da suke tunkarar manyan garuruwan da ke kan manyan tituna,” in ji shi.
Ya kuma kara da cewa hukumar za ta ci gaba da gudanar da ayyukan wayar da kan jama’a da tabbatar da tsaro domin dakile yawaitar haduran ababen hawa.