An sake samun wani mummunan hatsarin jirgin ruwa a Jihar Sakkwato, inda jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji da dama ya kife a ranar Alhamis a ƙaramar hukumar Shagari.
Ana tsoron cewa mutane da dama sun rasu yayin da wasu kuma suka ɓace.
- Tottenham Ta Ɗauki Xavi Simons Daga RB Leipzig
- Kungiyar Masana’antu Ta Yi Fatali Da Sake Gabatar Da Haraji Na Kaso 4 Na Kwastom
Mai Bai wa Gwamna Ahmed Aliyu Shawara kan Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), Aminu Liman Bodinga, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce wannan shi ne hatsarin jirgin ruwa na uku mafi muni a cikin wata ɗaya a jihar.
Ya bayyana cewa jami’an SEMA, NEMA, da NIWA sun isa waje domin ceto waɗanda hatsarin ya rutsa da su.
Shaidu sun ce jirgin cike yake da mata, maza, da yara, kafin ya kife a tsakiyar ruwa.
Wasu daga cikin fasinjojin sun yi nasarar yin iyo inda suka tsira, amma har yanzu ba a gano da dama ba.
Al’umma sun daɗe suna zargin irin waɗannan hatsari na faruwa ne saboda ɗauke fasinjoji fiye da ƙima, rashin saka rigar iyo, amfani da jiragen ruwa marasa inganci, da kuma rashin bin ƙa’idojin tsaro.
Duk da wannan, gwamnati ba ta ɗauki matakan tsaro ba.
A halin yanzu, magidanta a Shagari da ƙauyuka maƙwabta na cikin tashin hankali suna jiran labari game da ‘yan uwansu da suka ɓace, yayin da ake ci gaba da zaman ɗarɗar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp