Jiya Litinin, ma’aikatar harkokin aladu da yawon shakatawa ta kasar Sin, ta fidda bayani game da kasuwannin raya aladu da yawon shakatawa, a lokacin hutun bikin sabuwar shekarar nan ta 2024.
Kididdigar da cibiyar bayanai ta maaikatar ta fitar ta nuna cewa, a yayin hutun kwanaki 3 na bikin sabuwar shekara, mutane kimanin miliyan 135 sun yi tafiye-tafiye na yawon shakatawa a kasar Sin, adadin da ya karu da kaso 155.3 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokaci na bara, kuma adadin ya karu da kaso 9.4 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokaci na shekarar 2019.
- Adadin Wayoyin Salula Da Kamfanonin Kirar Su Suka Fitar A Kasar Sin Ya Karu Da 34.3% A Watan Nuwamba
- Xi Jinping Ya Gana Da Jakadun Kasar Sin Dake Kasashen Waje Wadanda Suka Dawo Beijing Don Halartar Taro
Kaza lika hakan ya sa an samu kudin shiga kimanin Yuan biliyan 79 da miliyan 730, a harkokin yawon shakatawa a kasar ta Sin, adadin da ya karu da kaso 200.7 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokaci na bara, wanda ya kuma karu da kaso 5.6 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokaci na shekarar 2019.
Har ila yau, a yayin hutun bikin sabuwar shekarar, an gudanar da ayyuka masu nasaba da aladu da yawon shakatawa yadda ya kamata a duk fadin kasar Sin.
A lokacin hutun, mazauna birane da kauyuka sun nuna kuzarin tafi yawon shakatawa, musamman ma zuwa wuraren wasa da kankara da na dusar kankara, a maimakon tafiya wuraren yawon shakatawa na gargajiya. A halin yanzu, mutane sun fi son tafiya wuraren shan iska cikin birane da wuraren wasanni na musamman.
Tsoffi da masu matsakaitan shekaru, da mazauna kauyuka, da kuma mutanen dake zama cikin kanana da matsakaicin birane, sun nuna kuzarin tafiya yawon shakatawa. Cikin wadanda suka yi yawon shakatawa, an samu karuwar adadin tsoffi, da masu matsakaitan shekaru, da mutanen dake zaune a kauyuka, da kuma mazauna kanana da matsakaitan birane, lamarin da ya yi muhimmin tasiri ga kasuwannin yawon shakatawa.
Bayanin da cibiyar bayanai ta maaikatar harkokin aladu da yawon shakatawa ta kasar Sin ta fidda, ya nuna cewa, cikin farkon kwanaki biyu na hutun bikin sabuwar shekarar, yawan mutanen da suka tafi yawon shakatawa daga yankunan karkara ya kai kaso 4.2 bisa dari, adadin da ya kai kaso 20 bisa dari bisa yawan alummar da suka yi yawon shakatawa a cikin kasar Sin, kuma adadin da ya kai matsayin da ba a taba gani ba a yayin hutun bikin sabuwar shekara. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)