Wani sabon rahoto daga Cadre Harmonisé (CH) ya bayyana barazanar ƙarancin abinci mai tsanani da ke tunkarar Nijeriya, inda aka ƙiyasta cewa kimanin mutane miliyan 33.1 za su fuskanci matsanancin rashin abinci da abinci mai gina garkuwar jiki nan zuwa tsakiyar shekarar 2025.
Wannan bincike, wanda gwamnatin Nijeriya ta gudanar tare da haɗin gwuiwar hukumar abinci da aikin gona ta majalisar ɗinkin duniya (FAO), ya nuna cewa zuwa Disamba 2024, an yi hasashen mutane miliyan 25, musamman a Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya, za su shiga matsanancin ƙarancin abinci.
- Faransa Ta Shirya Bikin Baje Kolin Hanyoyin Bunƙasa Kasuwancin Kayan Abinci A Nijeriya
- Kasar Sin Ta Bada Tallafin Abinci Ga Mabukata Da Na Kudin Karatu Ga Dalibai A Malawi
Rahoton ya bayyana rashin tsaro, da hauhawar farashi, da matsalolin yanayi, da kuma talauci mai tsanani a matsayin manyan abubuwan da ke haifar da ƙaruwar wannan matsala.
Mutane sama da dubu 514 da aka tilasta wa ƙaura a jihohin Borno, da Sakkwato, da Zamfara na fuskantar barazanar shiga mawuyacin hali na ƙarancin abinci zuwa tsakiyar 2025, tare da waɗanda wannan matsalar ta shafa a jihohi 26 da Babban Birnin Tarayya (FCT).
Lokacin ƙarancin abinci na shekara-shekara a Nijeriya na iya kara ta’azzara wannan matsalar, wanda zai sa wasu gidaje su shiga cikin yanayin ƙarancin abinci mai tsanani.
Wakilin FAO a Nijeriya, Kouacou Dominique Koffy, tare da jami’an gwamnatin Nijeriya, sun yi kira da a ɗauki matakan gaggawa, kamar bayar da tallafin abinci, shirye-shiryen ƙarfafa juriya, da taimako ga gidajen da ke cikin mawuyacin hali domin daƙile mummunar matsalar da ke tunkara.