Shugabar Hukumar Yaƙi da Cutar AIDS ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNAIDS), Winnie Byanyima, ta yi gargaɗi cewa kusan mutum miliyan tara za su kamu da cutar HIV nan da shekaru huɗu masu zuwa, sakamakon dakatar da tallafin da Amurka ke bayarwa a fannin kiwon lafiya.
Da ta ke jawabi a Geneva, Byanyima ta bayyana cewa matsalar za ta janyo aƙalla sabbin masu kamuwa da cutar guda 2,000 kowace rana.
- ‘Yansanda Sun Cafke Mutum 2 Kan Zargin Kashe ÆŠan AchaÉ“a Da Sace Babur ÆŠinsa A BauchiÂ
- Kamfanin Apple Ya Sanar Da Zuba Sabon Jari A Fannin Samar Da Makamashi Mai Tsafta A Sin
Ta ce dakatar da tallafin ya riga ya haddasa asarar ayyuka ga dubban likitoci da ma’aikatan jinya, lamarin da zai iya jefa rayukan mutane da dama cikin hatsari.
Tallafin da Amurka ke bayarwa ya taka muhimmiyar rawa wajen rage yaɗuwar cutar HIV, musamman a ƙasashen Afirka inda ake fuskantar matsalar sosai.
Misali, shirin PEPFAR (President’s Emergency Plan for AIDS Relief) wanda Amurka ke É—aukar nauyi, ya taimaka wajen ceton miliyoyin rayuka tun da aka Æ™addamar da shi a 2003.
Sai dai duk da yaba wa Amurka bisa irin taimakon da ta bayar a baya, Byanyima ta nuna damuwa kan yadda aka dakatar da tallafin kwatsam ba tare da shiri ba.
Wannan na iya haddasa koma baya a ƙoƙarin da aka shafe shekaru ana yi na rage yawan masu kamuwa da cutar, musamman a yankunan da ke fama da talauci da ƙarancin kayan kiwon lafiya.
Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa, idan ba a samu sabbin hanyoyin tallafi ba, yiwuwar ƙaruwar mace-mace sakamakon cutar HIV na da matuƙar girma.
Hakan na iya rusa nasarorin da aka samu a yaƙin da duniya ke yi da cutar.
Ana ci gaba da kira ga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin agaji da su ceto shirin da ke kare miliyoyin rayuka daga barazanar cutar HIV.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp