Jaruma mai tashe a Masana’antar Kannywood a yanzu, Firdausi Yahaya ta bayyana batutuwa da dama a wata hira da ta yi da TRT Hausa, har ma ta tabo batun yadda mutane da dama ke yawan tambayar ta cewa, yaushe ne za ta yi aure da kuma sauran wasu batutuwa.
Tunda farko dai, jarumar ta kara jaddada wa al’umma cewa; ita ‘yar asalin Jihar Sakkwato ce, sannan kuma tana matukar alfahari da hakan duk da cewa wasu ba za su yarda da hakan ba, ganin yadda take iya magana a yanzu ba tare da amfani da karin harshe irin na jikokin Mujaddadi ba, ko kuma rashin amfani da wasu kalmomi da sakkwatawan ke amfani da su yayin magana kamar Awo, Taho da sauransu.
- Kasar Sin Ta Harba Sabon Tauraron Dan Adam Na Gwaji A Kan Fasahar Sadarwa
- Sinawa Kimanin Miliyan 1.85 Za Su Rika Zuwa Yawon Bude Ido a Ketare Kullum Lokacin Hutun Bikin Bazara
Firdausi da take amsa tambaya a kan mene ne sirrin da yasa a yanzu furodusoshi ke sha’awar aiki da ita? sai ta ce, ba wani abu ba ne face irin yadda take yin kokari wajen yin duk wani aiki da aka ba ta a cikin shiri; ba tare da gajiyawa ba.
“A tunanina, irin kokarin da nake yi wajen yin aikin tukuru a duk lokacin da na samu kaina a cikin shiri, ya sa mafi yawancin furodusoshin ke sha’awar aikin da ni, sannan kuma babban burin da nake da shi a wannan Masana’anta ta Kannywood shi ne, yadda na shigo da kafar dama; wato na samu daukaka, Allah ya sa hakan ya dore har lokacin da zan samu miji; ni ma na shiga daga ciki kamar sauran mata ‘yan’uwana”, in ji ta.
Daga karshe, Firdausi ta yi karin bayani dangane da yadda mutane ke yawan tambayar ta, lokacin da za ta yi aure, inda ta amsa da cewa, in sha Allahu; duk lokacin da Allah ya kawo mata mijin aure, to babu makawa za ta ajiye harkar fim ta yi aurenta tare da mijinta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp