A jiya Asabar ne aka rufe bikin fina-finan cartoon na kasa da kasa na kasar Sin karo na 19, a birnin Hangzhou dake lardin Zhejiang na kasar Sin. Kuma bisa kididdigar da kwamitin gudanarwar bikin ya fitar, gaba daya, adadin mutanen da suka halarci bikin na wannan karo sun kai mutane miliyan 10 da dubu 810, cikin har da wadanda suka halarci bikin ta yanar gizo, yayin da mutane dubu 955 suka halarci taron kai tsaye, tare da shiga aikace-aikacen bikin.
An bude bikin cartoon na wannan karo a birnin Hangzhou ne a ranar 20 ga watan nan, kuma babban taken sa shi ne “babban birnin cartoon, kuma birnin da za a gudanar da gasar wasan motsa jiki ta nahiyar Asiya”.
Ya zuwa karfe 12 na ranar jiya Asabar, gaba daya, akwai kamfanoni da hukumomi 567 na kasar Sin, da na kasashen ketare, da kuma ‘yan kasuwa da masana guda 2,305, da suka halarci bikin. Kuma cikin kwanaki biyar na gudanar bikin, an kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa da darajarsu ta kai kudin Sin Yuan biliyan 1 da miliyan 485. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)