Mata masu shayarwa da kananan yara a Jihar Borno, sun fara bin gidan tururuwa suna neman abinci, sakamakon ta’azzarar rashin abinci da karuwar cutar tamowa.
Mazauna wasu yankuna a Jihar Borno da ma’aikatan kiwon lafiya, sun shiga damuwa game da karuwar yara masu tamowa a jihar.
- Jami’ar Franco-British International Ta Shirya Soma Aiki A Watan Oktoba – Shugaban Jami’ar
- Gwamnati Ta Janye Dokar Hana Fita A Kaduna Da ZariyaÂ
Abin da suka ce na da nasaba da rashin wadataccen abinci mai gina jiki ga mata masu shayarwa.
Bugu da kari rahotanni sun nuna cewa kananan hukumomi bakwai ne a jihar ta Borno, matsalar ta fi shafa.
Kananan hukumomin sun hada da Marte da Kukawa da Abadam da Guzamala da Kaga da Mobar da kuma Gubio.
Yaran da ke a wadannan yankuna sun dogara ne da tallafin da suke samu daga kungiyoyin agaji.
Wata mata da ke aiki a kungiyoyin agaji, Fatima Muhammed Habib, ta manema labarai cewa, a da mutane ba su san ana fama da wannan matsala ba.
”Da muka je daya daga cikin wadannan yankuna mun tarar rabin yaran garin na fama da matsalar abinci mai gina jiki, haka suma matan da ke shayarwa, za ka gan su duk a wahale babu wani abinci mai maiko ko kyau da suke samu suna ci ga shi kuma suna shayarwa.”
Ta ce idan har uwa ba ta ci ta koshi ba ta yaya za ta samu ruwan nono bare har ta shayar da danta?
“Saboda tsananin yunwa haka za ka ga mata na tona gidan tururuwa don samu abinci, haka mata ke kungiya suna yawo don neman gidan tururuwar da za su samu abinci.”
“Babban abin tashin hankali shi ne daji matan ke zuwa don su samo gidan tururuwar, ga rashin tsaro a wuraren ga macizai da dai sauransu.”
Ta ce suna kai musu taimako, amma taimakon ba lallai ya isa ba.
Cutar tamowa dai ta jima ana yaki da ita, musamman a yankunan Arewacin Nijeriya.