A wani rahoto da Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno, BOSEMA, ta fitar ta ce adadin wadanda suka mutu a sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai a garin Gwoza da ke Karamar Hukumar Gwoza a ranar Asabar zuwa yanzu ya kai mutum 18, inda aka tabbatar da mutum 19 kuma sun samu raunuka.
LEADERSHIP HAUSA ta ce jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, ASP Nahum Daso, a ranar Asabar ya tabbatar da mutuwar mutane 8 tare da wasu mutane 15 da suka samu raunuka a yayin harin kunar bakin waken.
- Mutun 6 Sun Mutu Harin Ƙunar Ɓakin Wake a Borno
- Boko Haram Sun Sace Wani Alkali Da Matarsa Tare Da Awon-Gaba Da Wasu Mutane A Borno
Kazalika, wani karin bayani da Darakta Janar na BOSEMA, Dr. Barkindo Saidu, ya fitar wanda aka rabawa manema labarai a ranar Lahadin ya bayyana cewa adadin wadanda suka mutu a daren ranar Asabar ya kai 18, yayin da 19 da suka samu raunuka daban-daban inda yanzu haka suna jinya a asibitocin Maiduguri.
Dr. Saidu, ya ce akan idonsa, da misalin karfe 3 na yammacin ranar Asabar, bam na farko ya tashi a Gwoza, wanda wata ‘yar kunar bakin wake ta tayar da bam a wajen bikin aure.
Ya kara da cewa sama da mutane 30 ne abin ya shafa tare da raunuka daban-daban inda wasu kuma suka mutu nan take.
Dr. Saidu ya ce bayan ‘yan wasu mintoci, an sake samun fashewar wani abun fashewa a kusa da babban asibitin da ke garin.
A safiyar Lahadi, wata majiya daga BOSEMA da ta nemi bukaci a sakaya sunanta ta ce, adadin yawan mutanen suka mutu na iya zarce 18 idan aka yi la’akari da girman raunukan da suka samu.
A gefe guda kuma wata majiyar ta yi zargin cewa sama da gawar mutane 25 aka dauko daga wurare uku kafin sojoji su rufe hedikwatar karamar hukumar tare da sanya dokar hana fita da yammacin ranar Asabar.
Wakilinmu LEADERSHIP HAUSA ya ruwaito cewa, Gwoza na daya daga cikin kananan hukumomin da ‘yan ta’addar Boko Haram suka kwace a baya inda suka ayyana ta a matsayin mallakin su.