Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya jajantawa al’ummar Patigi da ke karamar hukumar Patigi kan hatsarin kwale-kwale, inda ya kife da mutane, da dama sun mutu wasu kuma ba a gansu ba.
LEADERSHIP ta tattaro cewa, kimanin mutane 100 ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin kwale-kwalen da ya afku a kauyen Egbu da ke karamar hukumar Patigi a jihar.
An rahoto cewa, lamarin ya faru ne a ranar Litinin a lokacin da wadanda hatsarin ya rutsa da su ke dawowa daga wurin daurin aure a kauyen Egboti da ke makwabtaka da jihar Neja.
Majiyar ta kuma ce, kwale-kwalen na dauke da fasinjoji sama da 300 a hanyar dawowa daga wurin daurin auren kafin ya kife a kauyen Egbu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, Okasanmi Ajayi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, ya ce rundunar ta umurci jami’an ‘yan sanda na yankin Patigi da su tattara cikakken rahoto kan lamarin.
Gwamna AbdulRazaq, a wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaransa, Rafiu Ajakaye, ya ce, ya yi bakin cikin samun wannan mummunan hatsarin kwale-kwalen da ya dulmiye da mutane da dama.