Wasu rahotannin baya-bayan nan na cewa, ma’aikatar cinikayya ta kasar Amurka, ta shigar da wasu kamfanoni 43, cikin jerin sunayen kamfanonin da ta kakabawa takunkumin sayar musu kaya, ciki har da kamfanonin Sin 31. Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, Sin ba za ta amince da wannan mataki na Amurka ba, ta kuma bukaci Amurka da ta dakatar da yin amfani da irin wannan mataki, wajen matsa lamba ga kamfanonin kasar Sin.
Ban da wannan kuma, game da batun cewa Amurka tana shirin komawa cikin hukumar raya ilmi, kimiyya da al’adu ta MDD wato UNESCO, Wang Wenbin ya ce, fatan Sin shi ne Amurka ta sauke nauyin dake wuyanta bayan ta tsai da wannan kuduri, don nuna goyon baya ga ra’ayin cudanyar bangarori daban daban, da kuma sa kaimi ga yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa.
Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, bai dace a mayar da shiga wata hukumar kasa da kasa tamkar zuwa yawon shakatawa ba, wato a rika shiga ko fita yadda aka ga dama. Kana bai kamata a mai da kungiyoyin kasa da kasa a matsayin fagen takara a fannin siyasa ba, wato dai a rika neman jagorancin duniya, ta hanyar shiga kungiyoyin kasa da kasa. (Zainab)